Sani Ibrahim da akafi sani da Dan Gwari shahararren ɗan wasan kwaikwayon Hausa ne wanda ya shahara wajen yin Muryar Gwarawa.
An haifeshi a Sabon Garin Kaduna yayi karatun sa na Firamare a garin Rigasa, yayi karatun sa na Sakandire a garin Rigachukum.
Saboda yanayin rayuwa bai cigaba da karatu ba don haka ya shiga harkar wasan kwaikwayo a shekarar alif 1985 a wata ƙungiya mai suna Dr. Abubakar Imam dake garin Rigasa wanda a lokacin suke wasan kwaikwayo irin su daɓe.
Sun haɗu da marigayi Labiru Musa Dan Ibro a shekarar alif 1987 suka fara wasan Hausa tare. A cewarsa Dan Gwari marigayi Dan Ibro ne ya karfafa masa gwiwar da shawarar kwaikwayon gwari domin a cewar sa babu mai wannan baiwar ta kwaikwayon gwarawa a harkar fina finai.
Dan Gwari yayi fina finai nasa na kansa sama da 30 sannan kuma ya temaka wajen haɗa fin da dama.