Tarihin Jarumi Sadiq Sani Sadiq

0 1,213

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Sadiq Sani Sadiq da akafi sani da Gambo Uban Tani an an haife shi a ranar 2 ga watan Fabrairu shekarar alif 1981 a garin Jos dake Najeriya, ɗan wasan fim ne na Hausa da Turanci. A shekara ta 2012 yayi fim mai suna Blood and Henna, wani fim na Kudanci wanda Kenneth Gyang ya shirya tare da Nafisat Abdullahi da Ali Nuhu.

Yayi karatun sa na Firamare da Sakandire a garin Jos, ya kuma yi karatun aikin jarida wato masa communication a jami’ar Jos duka a Najeriya.

Sadiq Sani Sadiq

Yayin karatunsa na Sakandire yanada aboki mai harkar wasan Hausa mai suna Bello M Bello wanda hakan ya kuma bashi damar daɗa son harkar wasan Hausa.

Ya shiga ƙungiyar fina fina Hausa ta kannywood a shekarar 2004. Jarumin nada sha’awar zama ɗan wasan Hausa tun a karatunsa na Firamare.

Yasami lambobin yabo da dama dama ciki harda gwarzon shekara a shekarar 2012.

Sadiq Sani Sadiq yana da aure da ya’ya, matarsa itace ƙanwa ga tsohon Gwamnan jihar Katsina Shehu Sheme mai suna Murja.

Sadiq Sani Sadiq

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »