TAKAITACCEN TARIHIN MARIGAYI RABILU MUSA (IBRO)

0 5,530

An haifi marigayi Rabilu Musa Ibro a shekarar 1971. Ya yi karatun Firamare dinsa a Danlasan da ke cikin karamar hukumar Warawa. Sannan kuma ya yi Sakandare a Kwalejin horon malamai ta Wudil (Teachers College).

AIKIN GWABNATIN SA

Daga nan ne ya shiga aikin gidan Yari (Prison Service) a shekarar 1991. Ya yi shekara takwas Ya na aikin Gandiroba inda ya kai matakin insfekto, daga nan ne ya bari ya cigaba da sana’ar wasan kwaikwayo.

FARA SANAAR FIM DINSA
Rabilu Musa Ibro ya fara sana’ar Fim ne tun ya na aji uku na makarantar sakandare.

IYALANSA

Ya na da Mata da Yara hudu ko uku akwai : Jamila, Kubra, Auta.

Daga cikin yaransa akwai: Akwai Faisal, Jawahid, Lawiza, Abdul-Mummuni, Sannan akwai Asma’u, Annabe, Sa’adiyya, Akwai wani yaro kuma da ya Haifa ya sa sunan mai gidansa wato Baba Yaro.

Kafin Rasuwarsa Ya bayyana Ciroki a matsayin dan wasan hausa abokin sana’ar sa da ya fi burgeshi.

Da aka tambayi Rabilu Musa ibro dan wasan santimental da ya fi burgeshi sai yace “ Adamu Usher, ka ga wannan, yana bani sha’awa. Saboda ba shi da girman kai, ba zan manta ba lokacin rasuwar kulu da Yautai, tun daga farkon rasuwar mu na tare da su.” In ji Ibro.

Daga cikin dubunnan fina finansa ibro ya bayyana cewa ya fi son wadannan fina finai “Akwai Kauran Mata, Kowa Ya Debo Da Zafi, da kuma Mai Dawa.

Ibro ya bayyana ya fi son tuwon dawa a bangaren abincinsa, fannin sutura kuma sai yace “Na fi son yadi wanda zan shekara da shi ina gurzawa, ba in sa Shadda ba kwana biyu in ga tana kodewa.

Da aka tambayi Marigayi Ibro a lokacin ya na raye me ya fi bakanta masa rai a kan harkar sana’arsa sai yace“ Ni abinda yake bata mani rai kawai a wannan sana’a bai wuce rashin hadin kan ‘yan wasa ba.

MUTUWAR SA
Rabilu Musa Ibro Ya Rasu ranar 9 ga watan Disambar shekara ta 2014, ya rasu ya na da shekaru 43, a duniya. Allah ya kyautata makwanci.

GA WANI DAN KARAMIN SHIRI NA IBRO
Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »