Tarihin Aminu Muhammad Ahmad (Aminu Saira)

0 1,488

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Aminu Muhammad Ahmad wanda aka fi sani da Aminu Saira, an haife shi a ranar 20 ga watan Afrilun shekarar alif 1979 ɗan wasan fina finan Hausa ne na Nijeriya, darekta kuma marubucin labarina.

Mutane suna kallon shi a matsayin mai son kawo sauyi a masana’antar shirya finafinai ta Kannywood, sannan kuma kyakkyawan abin koyi ne ga sauran taurarin finafinan Hausa kasancewar shi mai ladabi ne, mai wayewa da tarbiyya.

Ɗaukakar Aminu Saira ta kuma Bayyana a masana’antar fina-finan Hausa bayan fitowar finafinan sa Jamila Da Jamilu a shekarar 2009, Ga Duhu Ga Haske a 2010 da kuma Ashabul Kahfi a 2014, wanda hakan ya ba shi lambobin girmamawa da kyaututtuka da dama ciki har da Babban Darakta na Shekarar wato:

  • Jurors Choice Awards, a cikin shekarar 2014.

Bayan fitowar fim ɗin Ashabul Kahfi, Saira ya fara aikin kaddamar da jerin bidiyon Hausa (Hausa Series) na farko a tarihin masana’antar finafinan Hausa, mai Suna Labarina, wadda a yanzu Shine ne fim din gida mafi kyau a Kannywood.

Fim ɗin Ashabul Kahfi da Baya Da Ƙura sune fina-finai biyu da suka fi kawo kuɗi, A shekarar 2016, Aminu ya zama fitaccen daraktan Kannywood a kowane lokaci kuma wanda kamfanin sa ya fi biya a tarihin masana’antar fim ta Kannywood.

RAYUWAR AMINU SAIRA:

Aminu saira

An haifi Aminu a Gwammaja, jihar Kano, dake Nigeria.

Aminu ya girma a cikin garin kano tare da kannen sa guda biyu wadanda dukkanin su na masana’antar ta Kannywood kuma ya samu karatun sa na firamare da sakandare da kuma manyan makarantu a Kano.

Yayi karatun Al-Qur’ani a kwalejin Aminu Kano Islamic and Legal Studies, Kano. Aminu ya bar aikinsa na dan kasuwa ya shiga masana’antar shirya fina-finai ta Kannywood a shekarar alif 2006 tare da fim dinsa na farko mai suna Musnadi wanda ya girgiza masana’antar.

Aminu Saira shi darakta ne, marubuci kuma furodusa a shirin Dare Da Yawa wanda aka shirya a 2007, da Jamila Da Jamilu wanda aka shirya a 2009, da kuma wanda ya fi so Ga duhu Ga Haske wanda aka shirya a 2010, wanda ya fito ba’a Musulmi ba daga baya kuma yakarɓi addinin musulunci.

Ya ci gaba da rubutawa da kuma ba da umarni fina-finai gami da Hausa Series na na farko kuma daya daga cikin ingantattun jerin fina-finan Hausa wato Labarina karkashin sunan sa, wato Saira Movies.

TASIRIN SA A KANNYWOOD

Kyakykyawar Rayuwar Aminu Saira ta sanya shi zama cikakken mutum a cikin masana’antar fim ta Kannywood.

  • Haka kuma Nafisa Abdullahi ta bayyana shi a matsayin daya daga cikin masu yi mata nasiha.

Tasirin sa ya karu a cikin masana’antar fim bayan fitowar fim din sa mai suna Sarauta a shekarar 2011, wanda ya karawa Ali Nuhu ƙima a harkarsa ta fim, sannan daga baya ya ci gaba da jan ragamar sa bayan fitowar fim ɗin Daga Ni Sai Ke da ‘Ya Daga Allah a shekarar 2014.

LAMBOBIN YABON DA AMINU SAIRA YA SAMU

NShekaraGirmamawaSassaFimSakamako
12013Entrepreneurship
Award
Best DiractorSpecial
Recoganition
Won
22013Kannywood/
AMMA/Award
Best movie
Diractor
Ɗakin AmaryaWon
320141st Kannywood AwordBest Director
of the Year
(Jurors Choice Awards)
Wata Huɗuwon
42014Kannywood/
AMMA/Award
Best Director
(Popular Choice Awards)
Ali Yaga Ali Won
520152nd Kannywood/
Mtn Awards
Best Director
of the Year
(Jurors Choice Awards)
Ashabu Khafi Da
Ali Yaga ali
won
6Kannywood/
AMMA/Award
Best Director
(Popular Choice Awards)
Baya Da
Ƙura
won

WASU DAGA DAGA CIKIN FINAFINAN AMINU SAIRA

ShekaraSunaMatsayiTaurariKamfani
2009Jamila Da
Jamilu
DaraktaMaishunku,
J Nagudu
Kamfanin
Saira.
2006MuanadiDaraktaSafiya,
Al-Mustapha,
Mai Shinku.
Kamfanin
Saira.
2007AlmajiraDaraktaMaishunku,
Safiya Musa,
A Shariff,
Al-Mustapha.
Kamfanin
Saira.
2007Dare Da
Yawa
DaraktaMaishunku,
Ali Nuhu,
Kubra Dako,
M Hiyana.
Kamfanin
Saira
2008Garin Mu
Da zafi
DaraktaAli Nuhu,
Zango,
M Booth,
Z Abdullahi
Kamfanin
Uk
Entermnt

ShekaraSunamatsayiTaurariKamfani
2009Mai Gidan
Zinare
Darakta Ali Nuhu,
Nagudu,
Maishunku.
Kamfanin
Saira
2010Ladidin
Baba
Darakta Ali Nuhu,
Zainab
Umar.
Kamfanin
Uk
Enternmnnt
2010JiddaDaraktaMaishinku,
Nagudu,
Ishaq
Sidi Ishaq.
Kamfanin
Square
Media
2010Dan SarkiDaraktaAli Nuhu,
Zainab U,
Hajara U,
Musa A.
Kamfanin
Kabugawa
2010Ga Duhu
Ga Haske
DaraktaA Zango,
Zainab A,
Zainab U.
Kamfanin
Saira
2010Miyati
Allah
DaraktaMaishunku,
Fati KK,
Binta Yhy.
Kamfanin
G-Top
2010Rai Da RaiDarktaMaishunku,
Rashida A,
Fati KK.
Kamfanin
T.M.A
2010BalarabaDarktaBaballe H,
A Zango,
S Gyale.
kamfanin
Square
Media
2010WaliJamDarktaA Zango,
Zainab A,
Audu Kano
Kamfanin
Uk Entermt
2010Mata Da
Miji
DarktaMaishunku,
Binta Y,
Fati K. K.,
Rufaida M.
Kamfanin
G-Top

ShekaraSunaMatsayiTaurariKamfani
2010Daɗin bakiDarktaMaishunku,
Jamila U.
Kamfanin
2011SaurtaDarktaAli Nuhu,
Rahma H,
Hadiza M,
Mai Kaba
Kamfanin
T.M.A
2011MalikaDarktaAli Nuhu,
Nafisa A,
Rikadawa,
Hadiza M.
Kamfanin
Saira
2011Laifin
Daɗi
DarktaKumurci,
A Zango,
Nafisa A.
Kamfanin
G-Top
2011Ban
Saketa ba
DarktaMaishinku,
Fati kk.
Kamfanin
Kabugawa
2011Maryam
Diyana
DarktaRahama H,
Hauwa M,
Ali Nuhu,
Sani Sadiq.
Kamfanin
Uk
Entmnt
2011AjnabiyyaDarktaMaishunku,
Zainab A,
Rahama H.
Kamfanin
Uk
Entmnt
2012MutallabDarktaAli Nuhu,
A Zango,
Nafisa A,
Carmain Mc,
Nakwango.
Kamfanin
Square
Media
2012Ƴar
Agadez
DarktaZainab A,
Maishunku,
Nafisa A,
A Zango
Kamfanin
Uk
Entmnt
2012Dan
Marayan
Zaki
DarktaNafisa A,
Sadiq Sani,
Rahama H,
Hadiza M,
Sadiq A.
Kamfanin
Saira

ShekaraSunaMatsayiTaurariKamfani
2012Kara da
Kiyashi
DarktaAli Nuhu,
Hadiza M,
B Nayaya,
Nafisa A.
Kamfanin
Uk
Entrnmt
2012Ban Sani
Ba
DarktaHadiza A,
Shehu H,
Shu’aibu L.
Kamfanin
T.M.A
2012Taron
Giwa
DarktaAli Nuhu,
Nafisa A,
Shu’aibu L.
Kamfanin
Asnanic
2012Kona GariDarkta
Ali Nuhu,
Maryam M,
Atete,
Waraka.
Kamfanin
T.M.A
2013FisabilillahDarkta Ali Nuhu,
Nafisa A,
Hadiza M,
Rikadawa.
Kamfanin
G-Top
2013LamirajDarktaRahama H,
Ali Nuhu,
Nafisa A.
Kamfanin
Saira
2013Ɗakin
Amarya
Darkta
Ali Nuhu,
Atete,
Tsamiya.
Kamfanin
Asnanic
2013Fari Da
Baƙi
DarktaRahama H,
Al-Amin B,
Ali Nuhu.
Kamfanin
G-Top
2013Farin DareDarktaAli Rabi’u,
Bello M Bello,
Sadau
Kamfanin
Uk
Entmnt
2014Ƙanin MijiDarkta Ali Nuhu,
Jamila U,
Nuhu A.
Kamfanin
Saira

ShekaraSunaMatsayiTaurariKamfani
2014Kisan GillaDarktaSani Sadiq,
Gabon,
Sadau,
Bello M Bello.
Kamfanin
Asmasan
Picture
2014Ashabul
Khafi
DarktaTahir Fagge,
Tijjani Frg,
Al-Amin B.
Kamfanin
Saira.
2014Daga Ni
Sai Ke
DarktaSadiq A,
Zaharadden S,
Sani Sadiq
Gabon,
Atete.
Kamfanin
Saira.
2014HaskeDarktaAina’u Ade,
Ali Nuhu,
Ali Rabiu,
Abbas Sadiq.
Kamfanin
Saira.
2014Kalamu
Wahid
DarktaNafisa A,
Sadiq Ahmad,
Ali Nuhu.
Kamfanin
Kabugawa.
2014Ƴa Daga
Allah
DarktaAli Nuhu,
Nafisa A,
Fati A,
Sani Saqid,
Hadiza M.
Kamfanin
Saira
2014Ali Yaga
Ali
DarktaAli Nuhu,
Hadiza Aliyu
Sani Saqid,
Jamila Umar.
Kamfanin
Kabugawa
2015Baya Da
Ƙura
DarktaAli Nuhu,
Nuhu A,
Sidi Ishaq,
Fati Washa,
Hadiza M.
Kamfanin
GG
2015Wani
Zama
DarktaYakubu M,
Jamila Umar,
Shehu H Kano
Kamfanin
Asnanic
2015Uwa Tafi
Uwa
DarktaAli Nuhu,
Hadiza Aliyu.
Kamfanin
Mikiya

ShekaraSunaMatsayiTaurariKamfani
2015Gidan
Kiyso
DarktaAli Nuhu,
Jamila Umar,
Fati Abdullahi
Kamfanin
Kabugawa
2016JarumataDarktaAli Nuhu,
Hadiza Aliyu,
Jamila Umar,
Waraka,
Nuhu A.
Kamfanin
G-Top
2016Kalo Ya
Koma
Sama
DarktaAli Nuhu,
Jamila Umar,
Baballe H.
Kamfanin
Saira

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »