Hadiza Aliyu wacce akafi sani da Hadiza Gabon an haifeta 1 ga watan Yuni 1989, ƙwararriyar wajen fim din wasan hausa. Tana daya daga cikin shahararrun yan wasan kwaikwayo a Kannywood.
Hadiza kan yi shiga irin ta mata a addinance. Sannan kuma bata fitar da tsaraicin ta a waje. Wajen tafiyar ta al’amura kuwa na rayuwa, Hadiza Gabon ba’a bar ta a baya ba, inda shima ta kasance daya tilo.
Hadiza tana aiki a matsayin jakada ga kamfanin MTN Nigeria da kuma kamfanin Indomie kuma ta samu kyautar lambar yabo (Jaruma) ta Kannywood wadda kamfanin MTN Nigeria ke daukar nauyi. A yanzu tana hidimar kafa gidauniyar HAG.
FARKON RAYUWARTA DA KUMA DANGINTA
An haife ta a Libreville, Jamhuriyar Gabon, Hadiza Aliyu ‘yar Malam Aliyu ce. A bangaren mahaifinta, Hadiza tana daga zuriyar Gabon ce, kuma a bangaren mahaifiyarta, asalin kabilar Fulani ne daga jihar Adamawa, Najeriya.
Hadiza Aliyu tayi makarantun firamare da sakandare a kasarta ta haihuwa. Ta rubuta jarrabawarta ta sakandare tare da burin zama Lauya, daga baya ta zabi Law a matsayin matakin karatun da ta fi so.
Ta fara karatun ta na jami’a a matsayinta na daliba, amma tilas ta fice daga makarantar saboda wasu batutuwan da suka kawo cikas ga karatun nata. An dakatar da karatun nata a wancan lokacin kuma hakan ya ba ta damar halartar makarantar difloma a Harshen Faransanci daga baya ta zama malamar koyar da harshen Faransanci a wata makarantar kudi.
FARA FIM DINTA
Hadiza Aliyu ta koma Kaduna daga Adamawa gaba dayanta a Najeriya bayan ta nuna sha’awar na shiga kungiyar fim din hausa wato Kannywood tare da dan uwanta.
Daga nan ne ta hadu da Ali Nuhu don neman taimakonsa wajen cikar burinta, inda ta fara fitowa a fim din Artabu a shekarar ta 2009
LAMBOBIN YABON DATA SAMU
Hadiza Gabon ta samu lambobin yabo dana girma kala kala a masana’antar Kannywood. Ciki harda Fitacciyar Jaruma a masana’antar Nollywood a shekara ta 2013 a fim din ‘Babban Zaure’ da kuma Jaruma a taron ban girma na biyu a masana’antar Kannywood wanda akayi a shekarar 2014 a fim din ‘Daga Ni Sai Ke’. Mai Girma Gwamnan Kano Dr. Rabiu Musa Kwankwaso shima ya samu baiwa Jaruma Hadiza Gabon lambar yabo a shekara ta 2013.
Jaruma Hadiza Gabon ta dauki lambar girmamawa daga Kannywood AWA 24 Film & Merit Award a shekarar 2015 a fim din ta na ‘Ali Yaga Ali’. Sai kuma taron African Hollywood Awards shima data samu na fitacciyar Jaruma a shekara ta 2016 a fina finan Hausa na nahiyar Africa a cikin yaren Hausa.
Hukumar Gidan Malamai da aka fi sani da Kano State Senior Secondary Schools Management Board ita ma ta karrama Hadiza Aliyu Gabon a shekara ta 2016 a bisa gudummawar da ta bawa ilimi a Jihar Kano karkashin Gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje. Sai kungiyar Start Up Kano ta karrama Hadiza a shekara ta 2016 a bisa babbar gudummawa akan bayar da jari ga marasa aikin yi.
ah , gaskiya karatun hadiza Gabon yanada mahimmanci sosai dukk macen datake sonkaratun lawya gaskiya jarumace sosai
Slm Hadiza barka da aiki Allah yataimaka ameen inasan kibani lokacin haduwa dke domin nunawa dunia