Tarihin Mawaƙi Nazifi Asnanic

0 824

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Nazifi Abdulsalam Yusuf wanda akafi sani da Nazifi Asnanic an haife shi a ranar 2 ga watan Fabrairun shekarar alif 1982, mawaƙi ne a Jihar Kano dake Nijeriya, marubucin waƙa, darakta, kuma furodusa.

An haifeshi kuma ya girma a garin kano. Nazifi Asnanic wanda masoya Waƙoƙin sa ke yawan kiran sa da mai Muryar Zinare, yana daya daga cikin haziƙan mawakan Hausa.

Ya samu lambobin yabo da nade-nade da suka hada da:

  • City People Entertainment Awards a matsayin fitaccen mawaki na shekarar 2014.

Ya kuma kasance cikin jaruman Kannywood da suka samu lambar yabo daga gwamnatin Jihar Zamfara dake Najeriya saboda gagarumin kokarinsu da gudummawarsu wajen hada kan al’adun Hausawa da kuma dorar da su.
Asnanic yana fitowa, yana kuma bada umarni a wasu daga cikin finafinan Hausa na Kannywood.

Mawaƙi Asnanic ya fara harkar waka ne a farkon shekarar alif 2000. A Shekarar Alif 2002, ya fara buga faifan sa na farko da wakoki 10 ciki har da Dawo Dawo.

Ya dauki hankalin daraktoci da Furodusa kamar irin su Ali Nuhu da Aminu Saira inda ya yi waƙoƙi ga kamfanin shirya finafinai na FKD da kamfanin finafinai na Saira a cikin fim din Ga Duhu Ga Haske da kuma Sai Wata Rana.

Nazifi Asnanic ya sake fitar da faya-fayai na waƙoƙin sa gida 10, kuma ya sayar da kwafi ɗinsu da dama a Nijeriya da duniya baki daya wanda hakan ya sa ya zama daya daga cikin mafiya nasara a Kannywood.

Baya ga kiɗa da waƙa, Nazifi yana shirya kuma ya bada umarnin finafinai da yawa kamar su:

  • Rai da Buri,
  • Shu’uma,
  • Ba’asi da sauransu.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »