TAKAITACCEN TARIHIN ALI NUHU

3 4,050

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

An haife Ali Nuhu Mohammed a 15 ga watan Maris 1974 ɗan wasan fim ɗin Najeriya ne, mai gabatarwa, darekta, ɗan rawa kuma marubucin fina finai. a cikin finafinan Hausa da turanci kuma ana kiransa da “Sarkin Kannywood” .

FARKON RAYUWARSA DA ILIMINSA

An haife Ali Nuhu ne a cikin garin Maiduguri na jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya. Mahaifinsa Nuhu Poloma dan Balanga ne a jihar Gombe da mahaifiyarsa Fatima Karderam Digema daga ƙauyen Bama na jihar Borno.

Ya girma a garin Kano,. Bayan kammala karatun sakandare ya samu digiri a fanin ilmin sanin ƙasashe, teku, birane, yawan jama’a wato (Geography), sannan yayi digirinsa na biyu a fannin zane-zane a jami’ar Jos. Ya yi aikinsa na bautar kasa a Ibadan, Jihar Oyo.

Daga baya ya halarci Jami’ar Kudancin California don yin karatun Fim da kuma adabin fina-finai.

FARA FIM DINSA

Ali Nuhu ya shigo masana’antar shirya finafinan Hausa a shekarar 1999 a matsayin dan wasan kwaikwayo kuma ya fito a fina-finan Hausa sama da 260 da kuma fina-finan Turanci guda 150.

Ya halarci shirin koyon fim ne a Makarantar Asian School of Media Studies in Noida, New Delhi, India

NASARORIN DAYA SAMU

Ali Nuhu na daya daga cikin jaruman fina finan Hausa wadanda ke gaba a wajen samun gagarumar kyaututtuka a masana’antar ta Kannywood dama ta mutanen kudancin Najeriya wato Nollywood.

Anan zamu kawo maku wasu daga cikin kyaututtukan da Ali Nuhu ya samu a harkar sa ta shirya fina finai na Hausa da Turanci.

 • Arewa Films Award – Best Actor – 2005.
 • 3rd Africa Movie Academy Awards – Best Upcoming Actor award – 2007.
 • The Future Award – Best Actor – 2008
 • Zulu African Film Academy Awards – Best Indigenous Actor – 2011.
 • Best of Nollywood Awards – Best Actor (Hausa) – 2012.
 • Nigeria Entertainment Awards – Best Actor – 2013.
 • Best of Nollywood Awards – Best Actor (Hausa) – 2013.
 • City People Entertainment Awards – Kannywood Face – 2013.
 • Kannywood Awards – Best Actor – 2014.
 • Leadership Awards – Best Artiste – 2014.
 • City People Entertainment Awards – Best Actor – 2014.
 • City People Entertainment Awards – Recognition Award – 2014.
 • Arewa Music and Movie Awards – Pride of Kannywood – 2014.
 • Arewa Music and Movie Awards – Best Actor – 2014.
 • 19th African Film Awards – Best Outstanding Actor – 2015.
 • Best of Nollywood Awards – Best Actor (Hausa) – 2015.
 • Kannywood Awards – Best Actor – 2015.
 • City People Entertainment Awards – Kannywood Personality – 2015.
 • Arewa Music and Movie Awards – Best Actor – 2016.
 • City People Entertainment Awards – Kannywood Face – 2016.
 • Arewa Creative Industry Awards – Entertainment Award – 2016.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

 1. […] tasamu shahara sosai a wani fim mai suna Mansoor wanda Jarumi Ali Nuhu ya bada […]

 2. […] Jarumin yasamu farin jininsa ne yayin fitawa a wani fim mai suna “Gamu Nan Dai” fim ɗin daya ɗaukaka shi a masana’antar kannywood ta hanyar Jarumi Ali Nuhu. […]

 3. […] fina-finan Hausa don shirya fina-finansa da kuma ‘yan wasan da suka fi karbar kudi kamar Ali Nuhu, Adam A. Zango da kuma Rahama […]

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »