Tarihin Jarumar Finafinan Hausa Nafisa Abdullahi

0 1,551

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Nafisa Abdurahaman Abdullahi wacce akafi sani da Nafisat Abdullahi wasu kuma su kirata da Nafisat sai wata rana, shaharariyar yan Fim din wasan Hausace kuma yar kasuwa mai daukar hoto.

HAIHUWARTA;


An haifi Jaruma Nafisat Abdurahaman Abdullahi a garin Jos dake jihar Plato a ranar 23 ga watan Janairun Shekarar alib 1992.

KARATUNTA;


Nafisat Abdullahi tayi karatunta na Firamari a makarantar Air Force Private School Jos, bayan gama makarantar tata ne saita koma garin Abuja inda a nan ne taci gaba da makarantar Gobnati ta Government Girls Secondary School, Dutse dake Abuja.

Nafisat Abdullahi bata tsaya a iya nan ba domin ta fadada iliminta har zuwa matakin Digiri inda tayi Jami’ar Jos, ta fita da shaidar Digiri na Theater Art.

SHIGA MASANA’ANTAR FIM;


Nafisat Abdullahi ta shiga Kamafanin samar da Fina-finafinana Hausa na Jarumi Ali Nuhu wato FKD Production dake Kano, da shekaru 18 a duniya, yayinda ta fito a Fim dinta na farko mai suna SAI WATA RANA a shekarar 2010. Fim din da ya haskaka kuma ya daukaka Jaruma Nafisa Abdullahi.

Nafisat abdullahi
Nafisat

DAKATAR DA ITA DAGA SHIRIN FIM;


A watan June din shekarar 2013 ne dai aka dakatar da Jaruma Nafisat Abdullahi daga masanaantar fim na tsawon shekaru 2 sakamakon wani haramtaccen taro da masoyanta suka hada, saidai an yafewa Jarumar yayinda aka dawo da ita a wata biyu bayan dakatarwar, hat tafito a wani shirin fim na Kamfanin Aminu Saira mai suna KALAMU WAHID da kuma “YA DAGA ALLAH

Nafisat Abdullahi ta mallaki shagon saida kayayaki wato Nahaz Brand (Boutique) , sai kuma Kamafanin shirya fim Maisuna Nafs Entertainment Ltd, yayin da ta samar da Fim din GUGUWAR SO a 2016 sai kuma YAKI A SOYAYYA a 2018.

Nafisat Abdurahaman Abdullahi tasamu kyaututuka da dama kasancewarta Jaruma a fim inda tasamu Gwarzuwar Jaruma a shekarar (2015) Afro Bollywood award , MTN award (2016) da kuma AMMA award (2017).

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »