Takaitaccen tarihin Shaick Abdulwahab Abdullah.

0 3,115

Shaick Abdulwahab Abdullah, An haife shi ranar 28 ga watan Agusta na shekarar Alif 1953, wanda yay dai dai da Juma’a 17 ga watan Zul-Hijjah shekara ta 1373 Miladiyya, a ƙasar Togo.

Malamin, Bawangare ne, ya tashi ne a hannun Limamin Waje da ke birnin Kano, Imam Umar.

Shaick Abdulwahab Abdullah Ya soma karatu a wurin yayan mahaifinsa mai suna Imam Alhaji Yahya. Daga bisani ya yi karatu a wurin babban malami marigayi Imam Ɗan’ammu da ke birnin Kano.

Yawancin karatun Malamin da yayi ya shafi Riyadus-salihin da kuma Hadisai.

Ya yi karatun littafin Nahawul Wadi na 1 zuwa na 2 a wurin Sheikh Nasiru Kabara, Sheikh Shehu Maihula ya koyar dashi Askari.

Shiekh Abdulwahab ya ce lokacin yana matashi ya yi wasa irin wanda matasa suke yi kuma ya saurari waƙoƙin turawa irin na James Brown da na ƙabilar Igbo da na larabawa “saboda waƙoƙi suna ɗaukar hankalin yaro.”

Sai dai ya yi gargaɗi da matasa da kada su bari waƙoƙi su janye musu hankali “domin suna maye gurbin karatu.”

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »