BARMANI CHOGE
Hajiya Sa’adatu Aliyu (Barmani Choge), na daya daga cikin shahararun mawakan baka na Hausa dake Arewacin Najeriya, wadda kafin rasuwarta tayi Wakoki sama da guda dari. Kuma yawancin wakokin nata takanyi ne akan fadakarwa da kuma zaburar da Mata akan zamantakewa suda Mazajensu.
Ada mawakiyar tana bin mawaka ne donyin kida daga bisani kuma saita fara rera wakar kanta, kuma takanyi waka ne a wurin biki ko wani taro.
Rayuwarta
An haifi Sa’adatu Aliyu da akafi sani da (Barmani choge), a shekarar alib 1945 a kauyen Gwaigwayi, dake karamar hukumar Funtua ta jihar Katsina a yanzu.
Karatunta.
Mahaifinta Malami ne don haka Choge tasamu ilimin Addinin Isalama dai dai gwar gwado a wurin mahaifinta.
Aurenta.
Barmuna Choge ta auri Alhaji Aliyu tana da shekaru 15 a duniya, haka zalika shima Alhaji Aliyu mawaki ne a bangaren Garaya, ta haifi yara 12 da Alhaji Aliyu.
Alhaji Aliyu ya rasa a shekarar alif 1991, Choge ta kuma yin aure inda ta auri Alhaji Bello Kansil, a shekarar alif 1995.
Fara Wakarta.
Ta fara waka ne tun tana shekara 27. Tana daya daga cikin fitattun mawakan Hausa daga Arewacin Najeriya. Babban sakonnin wakarta shine mata su tashi su haskaka a wannan duniyar da maza suka mallaka.
Barmuna Choge ta rasu ranar 2 ga watan 3, 2013 sakamakon rashin lafiya, ta rasu tabar yaya da jikoki.