Yadda Zaki Shirya Spring Rolls

0 1,528

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Spring Roll daddan abinci ne wanda za’a iya yiwa baki ko wurin wani katafarrn biki,

Sannan Spring Roll Uwargida tana iya yiwa mai gida da yaran gida suci donjin dadinsu.

Abubuwan da Zaki Bukata.

 • Fulawa yadda ya sauwaka,
 • Man Gyada,
 • Ruwa,
 • Karas,
 • Albasa,
 • Attarugu,
 • Tafarnuwa,
 • Kabeji,
 • Koren Tattasai,
 • Korin,
 • Kayan da zai kara miki dan-dano,

Yadda Zaki Hada

A samu kwano sannan a zuba garin fulawa da ruwa, hadin yadanyi ruwa ruwa. Sannan a samu kasko a zuba man gyada kadan sai a dinga zubawa ana kwashewa, kamar yadda akeyin waina. Ayita da fadi kuma falai falai. Kuma kada ta soyu rakayau.

Spring Roll
yadda zaa zubata

A kankare karas a yanka shi kanana tare da kabeji a wanke a ajiye a gefe, sai a jajjaga tafarnuwa da attarugu. A yanka albasa da korin da kuma tattasai.

A dora tukunya a wuta sai a zuba karas da jajjagen attarugu da yankakken kabeji da albasa a soyasu yadda ya kamata. Sannan a dauko magi da korin a zuba har sai ya dan soyu sai a sauke a bari ya huce.

Bayan ya huce sai a dauko wannan wainar fulawar da aka ajiye, a dinga dibar cokali daya ko biyu na hadin ana zubawa a kai (Kamar yadda ake sa nama ko kifi a Miti Fayib) sannan a nade bakin a kalmashe.

Spring rolls
yadda zaa nadeshi bayan ansa kayan hadin

Bayan angama sassawa sai a kawo Man Gyada a zuba a kasko sai dora a wuta a soya har sai ya yi kamar ruwan kasa sannan a sauke.

Abin Lura:


Zaki iya yin wannan hadi don saidawa ga Jama’a don samun yan chanji.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »