TAƘAITACCEN TARIHIN ALH. HASSAN WAYAM MAI KUKUMA

1 4,967

An haifi Alh. Hassan Wayam a wani gari mai suna Gwadda, wanda kuma ake kira Bakin Ruba, a ƙasar Maradun ta Jihar Zamfara, a cikin 1956.

Mahaifin sa, Mal. Muhammadu, Babarbare ne. Mahaifiyar sa, Halima, Bafulatana ce. Sana’ar mahaifin ita ce sassaƙa, amma wani lokaci ya kan yi wa Fulani kiɗan kotso jefi-jefi.

Ya na yaro ƙarami, sai mahaifin sa ya koma wani gari mai suna Ƙunci da zama, can gabas da birnin Gusau.

Da Hassan ya ɗan data, sai ya koma Mayanci, nan kusa da Gusau, ya zama yaron kanikawa. To Mayanci bariki ce sosai a lokacin, ga karuwai da ‘yan caca da sauran ‘yan duniya. A nan sha’awar sa da kaɗe-kaɗe ta yi zurfi, musamman kiɗan kukuma. Amma bai fara koyo ba sai da ya koma gida Ƙunci. A can ya fara ɗinka kukuma da hannun sa. A duk lokacin da ya samu lokaci ya kan goga abar sa da hannun sa, amma a ɓoye.

Da ya ƙara wayo, sai ya sake komawa Mayanci, ya zama yaron wata mata, ya na wasa a gidan ta. To sojoji na yawan wucewa ta Mayanci, kuma su kan yada zango a can su ci abinci ko ma su kwana. Ta haka ne ya haɗu da wani soja mai suna Ali Barau, wanda ya buƙaci matar nan ta ba shi Hassan ya tafi da shi Zariya. Ta ce, “To ga shi nan amana.”

Ali Barau ya kai Wayam Zariya a cikin 1969, ya aje shi a gidan sa da ke Unguwar Kanawa. Duk yamma sai ya ɗauke shi ya kai shi barikin soja, ya riƙa yi wa sojoji wasa.

Dalilin zuwan shi Zariya kenan.

(Wannan tsakure ne daga wata hira da na sa wani wakili na, Usman Modibbo, ya yi mani da Hassan Wayam a cikin shekarar 1992, lokacin ina Editan mujallar Rana ta kamfanin Hotline, Kaduna. An buga hirar a cikin mujallar ta ranar 19 ga Oktoba, 1992, shafi na 17 da na 18. Modibbo ya yi Kwamishinan Ilimi na Jihar Kaduna, kuma yanzu farfesa ne.)

An ɗauki waɗannan hotunan na Alh. Hassan Wayam shekaranjiya a wajen bikin Dakta Ilham, ɗiyar Ɗanmalikin Kano, Amb. Ahmed Umar, a Kano. Allah ya ƙara masa lafiya da nisan kwana, amin.

Wakar Alh. Hassan Wayam

Allah yayi wa Hassan Wayam Rasuwa ranar asabar wanda yayi dai-dai da 24 ga watan Oktoba na shekarar 2020.

Daga Ibrahim Sheme

  1. Mallim Shuaibu says

    Allah ya rahamche shi

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »