TARIHIN DR. MAMMAN SHATA KASHI NA 3

0 7,705

WANNAN SHINE CIGABAN TARIHIN DR MAMMAN SHATA KASHI NA UKU

Wakar da Bawan yayi: 
Ado Dan Ma’inna goshin Jirgi kanen Barau’,

Itace tazo iri daya da wata  waka da Shatan ya taba yiwa Akawu Na Guga mai Biri da Barewa’,inda shi kuma yake cewa:’

Jefa kidan Na Guga koba girma da arziki’.

Daga baya kuma ya dauki amshinta yayi wa Bawa Janke direba na Musawa, inda yake cewa: 

Jirgin sama Bawa Tashi koli ka tsere na Laraba

Yayiwa direbobi da dama wakoki da salon wannan amshin. 

Daga baya ya dauki irin amshin kuma yayi wa su Bello Maitama da wani direba Dan Kaura wakoki. Shata bazai taba mancewa da Muhammadu Dankura sarkin Bege makadin sarkin Daura Abdulrahman ba,saboda bashi ma da babban aboki cikin makada kamarsa. Shima Dankura mai basira ne kwarai. Ya taba yiwa Sarkin Daura Abdulrahman ubangidansa wata waka mai shigen ‘Sadauki Shehu Magajin Mamman’ irin ta Shata. Kada a manta cewa Shata yayiwa manyan iyayen gidansa irin su Sardauna Gamji(1957), Haru Dan Kassim Kano(1956), marigayi hakimin Musawa Usman Liman (1952) da dai wasu da dama wakoki da irin wannan amshin.

Ya’u wazirin Shata shine babban yaron makadin, da suka hadu a Bakori cikin 1943. Amma a sannan Ya’u makadi ne mai zaman kansa. Sai a cikin 1959/1960 suka hade da Shatan, lokacin shi kuma ya taso daga Kano. Shima Ya’u fasihi ne matuka, don yama yi wasu wakoki wadanda sukayi kamanni da wasu wakokin Shatan. Kafin kuma su hade ya sha daukar wasu kalmomin Shatan yana gina nasa, kamar daga wakokin:

Soja iyalin Gwamna’(1967), 
Dan Leko Baban Leko’(1966), 
Tijjani Hashim Dan-iya’(1986), 
Don sallah da salatil fatihi(1962), 
Haji Iro Babangida’(1985), 
Ya Alhaji Babba Dan kamasho’(25/12/1980). 

Har karshen rayuwarsa Shata ya samu biyayya daga mawaka danginsa da dama. Saboda kashi 95 na mawakan Najeriya da ma wajenta suna aron kalmomin Shata dama wakokinsa suna gina nasu kalmomin wakokinsu. 

Sani mai kuntigi Gusau wani mutum ne da yayi yayi a Da. Shima ya ari wasu kalmomi daga Shata ba ma dai irin wakokin Bakandamiya

(alo-alo mai ganga ya gode (1959/1960),
da
Dan Zabarma ya kyauta, Dan Zabarma yallabai’(1961),
 da kuma
Yallabai yallabai yallabai ‘yar kankanuwa kankane’(1955) 

Duk wakokin Sani mai kuntigi Gusau ne asalin su. Ya’u Wazirin Shata yace saboda shima mai hazaka ne wasu wakokin sa sunyi kamanni da na Shatan. A zamanin yaki(1967-1970) Ya’u yayi wakoki na siyasar kasa.

Ba wani gidan rediyon da yafi fifita Shata fiye da gidan rediyon Tarayya na Kaduna. Musamman da makadin ya tafi Nijar a cikin 1959 akayi fira dashi akace wai yayi wa Sardauna wani tsokaci da baiyi wa mutanen NPC dadi ba. To wannan Magana ita tasa Shata yayi ban iska da wadanda ke dasawa dashi cikin ‘yan gidan sarautar Kano dama wasu jama’ar NPC. 

Alhali kage ne sukayi masa da kuma haushinsa da suke ji. Suka fusata suka juya masa baya. To Wamban Daura Bashar shi yayi ta kokari har ya daidaita Sardaunan da shi Shata. 

Tun cikin shekarun 1950 jami’o’in kasashen Turai da Amurka suka fara nazarin wakokin makadin. A wasu jami’o’I a Jamus ana nazarin wakokin Mamman Shata. A Jami’ar Kalifoniya ma wasu turawa kusan su 6 sunyi nazarin mawakin, in ka debe manazartanmu na gida, irin su Abdulkadir Dangambo da Farfesa Danbatta, wanda a cikin 1975 ya rubuta kundin digiri na 3 a jami’ar Indiyana, Amerika akan wakokin makadin. A shekarar 1972 shugaban kasa Janar Yakubu Gowon ya aika aka kirawo shi daga kasar Nijar, suka hadu a Kano ya gaisheshi ya bashi lambar yabo.

Ranar 15/10/1976 ma gwamnatin tarayya ta bashi lambar yabo mai suna MON, shi da Garba ABCD(shi kuma aka bashi lambar OFR). Cibiyar tunawa da James Coleman na Jami’ar Kalifoniya ma ta bashi lambar yabo sa’ilin da ya ziyarci can a cikin 1989. Akwai ma kananan lambobi da kungiyoyi suka bashi a garuruwa kamar Funtuwa da Kano da dai sauransu. 

Kashe maigirma Sardauna a cikin 1966 yasa wakokin Shata sun dauki wani sabon salo, na yi wa sojoji da ‘yan boko wakoki don basu kwarin gwuiwa don a tafi bakin daga. Don sai da aka kashe su Sardauna dasu Abubakar Tafawa Balewa muka fahimci a Arewa an barmu a baya. Wakokin Shata suka zaburar da ‘yan Arewa. 

An tsakuro wannan ne daga littafin Aliyu Ibrahim Kankara, mai suna ‘Mahadi Mai Dogon Zamani: Shata Da Kundin Wakokinsa’. 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »