Tarihin Marigayi Gambu Mai Wakar Barayi.

0 5,537

An haifi Alh. muhammad Gambo da akafi sani da Gambu a garin fagadan dake karamar hukumar Jega a jihar Kebbi a Najeriya. Gambu tun tasowar yarintarsa yana da rashinji ga kuma rashin tsoro.

Asalin sunan Gambu shine Muhammad Gambo, tun a wacen lokacin wasu kan kirashi da Gambu Kasancewar rashin iya fadin sunan Gambo din kai tsaye.

Mahaifin Gambu shahararren Malami ne, yayin da shikuma Gambu ba ruwansa da son gadon maihaifin nasa don haka nema Gambu kandauki kayan harbinsa a kullum ya tafi Jeji harbin Tsuntsaye da kuma sauran namun Daji.

Duk lokacin da Gambu ya samo Naman Dajinsa Sai ya taho gari ya saidawa da masu caca, haka kuma shima a nan zaiyi zamansa.

Gambu ya fara mu’amala da barayi ne a wurin yin caca, kasancewar duk lokacin da Gambu yay farauta to a gurin yake zama har zuwa dare. Wannan dalilin ne yasa Gambu ya fara sanin barayi masu tare Hanya, da masu fasa shaguna dadai sauransu.

Gambu kan ambaci Kulu a cikin wakokinsa ne saboda ita Kulu itace matarsa ta farko da mahaifiyarsa ta aura masa, don haka yake sonta tare da mutunta ta kasancewar mahaifiyarsa ce ta zaba masa ita.

Alh. Gambu ya rasu ranar Laraba 18 ga watan agusta 2016, ya rasu yana da kimanin shekaru 73 a duniya. yabar mata 4 da “Yaya dakuma jikoki masu yawa.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »