Tarihin Marigayi Umar AbdulAziz Baba Fadar Bege.

0 16,405

HAIHUWAR SA


An haifi Umar Abdul-Aziz Baba da akafi sani da (Fadar Bege) a garin Garko karamar Hukumar Wudil a da, wanda a yanzu tazama Karamar Hukuma mai zaman kanta a Jihar Kano, a ranar Alhamis a shekarar alib 1974.

Mahaifinsa Mal Umar, mai Unguwa ne a wani kauye dake garin Garko, bayan rasuwar mahaifin Fadar Bege lokacin yana dan shekar hudu (4) sai suka dawo Karamar Hukumar Wudil da zama shida mahaifiyarsa mai suna Malama Hadiza, kasancewar dama aikine yakai mahaifin nasa na Mai Unguwa garin na Garko lokaci da take hade da karamar hukumar Wudil.

FARA KARATUN ALQURANIN SA.


Fadar Bege ya fara karatun Alonsa ne a wata makaranta mai suna MAKARANTAR MALAM YAYA, a wurin wani mashahurin Malami dake cikin Karamat Hukumar Wudil mai suna Alaramma Malam Musa Yaya, wanda a yanzu haka shine shugaban Malamai na Karamar Hukumar Wudil.

FARA KARATUN BOKONSA.


Fadar Bege ya fara Karatunsa na Primary a Wudil Special Primary School a shekarar alif 1981, ya kamala karatunsa na Primary a shekarar alif 1986.

Sanan ya tafi Makarantar Koyan Kasuwanci dake Wudil, wato Government Secondary Commercial School Wudil a shekarar alif 1986, ya kuma kammala karatun a shekarar alif 1992.

Fadar bege bai tsaya a nan ba bayan kammala karatunsa na Sakandire, saikuma ya famtsama akan neman karatun adini iri daban daban a gurin Maluma masu tarin yawa, na ciki da wajen garin wudil, a karshe yazama shima mai bada karatu a Islamiya dake garin na wudil.

SANA’O’IN DA YAYI.


Marigayi Fadar Bege yayi sana’o’i da dama daga ciki har da wacce akasan duk wani dan wudil da yinta wato sana’ar dinkin Kwado Da Linzami,

Sannan marigayi Fadar Bege yayi sanar Tireda bai tsaya a iya nan ba yayi sanar daukar hoto.

Sanan yana hadin gwiwa da mahaifiyarsa wajen sana’ar Shinkafa.

FARA YABONSA GA SHUGABA (SAW).


Marigayi Fadar Bege yafara buga Mandiri ne a wata Kungiya mai suna Fitiyano.

Kasancewar basirar da Allah yabawa marigayi fada a harkar sai abokai suka fara bashi shawarar cewa ya fara rera kasidunsa na kansa, kasancewar a wancen lokacin duk inda ake maulidi yakanje ya rera wakar yabon Annabi (SAW) wace marigayi Alhaji Ahmad Rufa’i ya buga mai Suna SALLALLAH.

KASIDARSA TA FARKO DA YAFARA.


Bayan shawarwari da akayi ta bashi na daga yanuwa da abokan arzuka kan ya fara wakar kansa, Allah cikin ikonsa sai fara yin waka mai taken SAYYADI NASOKA YA SHUGABAN ALUMMA BABU YAKAI YA SHUGABANA, a shekarar alib 1992 wacce aka kaddamar a karamar hukumar Wudil Unguwar Kofar Fada bakin Jan-bulo, wanda Wakar tasamu zuwan babban sha’iri daga cikin birnin Kano wato Alhaji Sani Mai Sa’a ya kaddamar da wakar.

KOMAWARSA CIKIN BIRNIN KANO
Fadar Bege ya koma cikin Birnin Kano ne a shekarar 2000, domin kara fadada iliminsa na addinin Islama, inda a nan ne ya gamu da babban shehin malamin cikin birnin Kano wato Sheick Sharif Sani Jambulo.

WAKOKIN DA MARIGAYI FADAR BEGE YAYI.


Acikin zantawar da shafin Alummar Hausa yay da babban amininsa dake karamar hukumar Wudil wato Komared Aminu Mamanu Wudil, ya shaidawa Alummar Hausa cewa Wakokin marigayin suna da matukar yawa don kuwa koshi kansa Marigayi Fadar Bege baisan iya adadin wakokinsa ba.

Amma daga cikin Wakokin nasa ya bayyanawa Alummar Hausa wadanda sukafi shahara a wurin mutane, wadanda suka hada da:

  • Labbaika Rasulillah
  • Farkon Mafadi,
  • Ya Mustapha Zuljudi,
  • Assalamun-Alaika,
  • Aahalan Wassahalan,
  • Dan Asali,
  • Annabi Ni Ina Gaida Kai,
  • Maula Inyass,
  • Lamuni Nake Nemah,
  • Mai Babban Masallaci,
  • Nagaban Hankali,
  • Takalminka Yafi Kowa,
  • Murhun Gidan Annabi,
  • Mai Cikar Asali Ne,
  • Mahamudu Ma’aiki Na

RASUWAR SA.


Fadar Bege ya rasu a shekarar 2013, sakamakon rashin lafiyar da ya kwanta a asibity. Yabar mata da yara biyu. Allah ya jikansa da rahama yasa Aljannah tazama makoma tare da dukkan muslaimai baki daya.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »