Garin Wudil na ɗaya daga manyan garuruwa a jihar kano kuma gari ne mai ɗauke da tarihi, don haka muka ga dacewar taskance kaɗan daga ɗumbin tarihin wannan gari.
Ance wani maharbi ne ya sari garin, shikuwa daga Katsina ya taso. Tana iya yiwuwa Muhammadu sunansa, ko kuma Daudu, amma dai an tabbatar shine na farko da yazo ya zauna a wannan wuri inda garin wudil yake a halin yanzu.
Ko da yake, da fari ance acan tsallaken ruwa ya soma zama, amma sai yayi tunanin yin amfani da ruwa wajen kare kansa da garin da zai kafa daga mahara kasancewar wancan lokaci ana cike da yake-yake da kamen bayi, don haka ya tsallaka ruwa sannan ya kafa Bukkar sa yana mai cigaba da sana’ar sa ta farauta a dajin dake kewayen kogin wudil.
Sannu a hankali mutane matafiya masu zuwa neman ruwa suka rinka sauka a kusa dashi. Tun wasu na sauka su ɗanyi kwanaki sannan su tashi izuwa inda suka dosa, har kuma aka samu waɗanda suka mayar da wajen kachokan wajen zama tamkar shi. Akan haka akace gungun wasu fulan Joɓawa suka riski wannan maharbin tare da zama kusa dashi. Daga baya kuma sai shugabancin garin ma ya koma hannun su.
Sunan wudil ya samo asali ne daga wata Aljanna da aka tabbatar tana zaune a gidanta dake cikin tsakiyar wannan ruwa na Wudil. Ana kiranta da suna ‘Uwar Wudil’.
Babu tabbacin lokacin da aljannar ta soma zama acikin ruwan, amma dai an tabbatar da cewa har yanzu tana nan tare da ahalinta.
Ance ita fara ce doguwa mai siffar balarabiya, gashinta har gadon baya yake, kuma bata cutar da mutane, domin abaya takan shiga cikin garin Wudil ta yadda har mutane kanci karo da ita ba tare da ta razanar dasu ba. Ansha kuma ganinta a sauran garuruwa dake jikin wannan kogi na wudil.
Aljannar Wudil tana da tsohuwar alaka da mutanen garin Wudil.
Domin an samu cewar tana taimakon garin wajen samun kariya daga dukkan sharri tare kuma da yin galaba a yakunan da duk garin zai tunkara. Ance abaya, manyan gari na zuwa bakin kogi su yanka shanu, raguna ko tumaki sannan su sanar mata da abinda ya tasowa garin misalin yaƙi sannan sai azo a tafi. Ita kuma aikinta ne tayi duk mai yiwuwa wajen ganin buƙata ta biya.
Wannan abu yana daga abinda Mallam Bakatsine ya ƙyamata tare da riƙa a matsayin hujjar yin jihadi a zamanin Shehu Usman Danfodio. Don haka ance da lokacin hijira yayi, sai mabiya Shehu Usmanu dake kano suka tafi wani waje da ake kira Kwazazzabon Ƴarkwando, amma shi Mallam Bakatsine sai ya fita kano ta gabas yaje garinsu Utai ya ɗauki iyalinsa sannan ya ƙarasa garin wudil, inda ya yada zango a wani wuri da ake kira Nagge, anan ya tara runduna tare da zuwa buga yaƙi da garin Gaya inda ya ƙwace iko dashi.
Duk da kasancewar a lokacin Garin Wudil zagaye yake da ganuwa da kuma ɗumbin jarumai, kuma karkashi Sarkin Kano Alwali amma babu labari mai nuna cewa sarakunan wudil sun yaƙi Mallam Bakatsine, ance hakan baya rasa nasaba da kasancewar a zamanin Fulani ke mulkin garin kuma suna da alaƙa dashi, don haka suka mara masa baya har ya cimma burinsa.
Ana kiran sarautar Wudil da suna Ɗan Daudu, kuma garin yana can gabas da garin kano.
Marubuci:
Sadiq Tukur Gwarzo