Yadda Ya Kamata Ayi Gaisuwar Sallah

0 113

Gaisuwar sallah ana yintane da kowane lafazi halastacce, lafazin da yafi falala shine TAQABBALALLAHU MINNA WA MINKUM domin itace aka ruwaito daga sahabbai.

An ruwaito daga jubair bin nufair yana cewa “sahabban manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam sun kasance idan suka hadu da junansu ranar idi, suna cemusu taqabbalallahu minna wa minkum”. Ibn hajar ya hassana isnadinsa acikin Fathul baari.

An tambayi imam malik rahimahullah shin akwai laifi mutum ya yacewa dan uwansa bayan sallah idi, taqabbalallahu minna wa minkum wa gafarallahu lana wa lakum, shi kuma dan uwan ya mayar masa da makamancin hakan?? Sai imam ya amsa da cewa “babu laifi hakan”. Almuntaqa sharhul muwadda.

Shaikhul islam ibn taimiya yace”gaisuwa ranar idi, mutum yacewa dan uwansa idan ya hadu dashi bayan sallah taqabbalallahu minna wa minkum, wa a halahullahu alaika, dama wasun irin wannan gaishe gaishen, an ruwaito su daga wani sashi na sahabban manzon Allah, sannan wasu daga cikin imamai sunyi rangwame gameda aikatashi, kamar imam Ahmad ya waninsa, sai dai shi imam Ahmad yace “ni bazan fara yiwa kowa ba, amma idan wani yamin zan amsa masa saboda amsa gaisuwa wajibine” Amma fara ita wannan gaisuwar babu wata sunnah da tayi umarni da ita kamar yadda batayi hani da ita ba, wanda yayi yanada magabata akai, wanda ma yakiyi shima yana da magabaci akai”. Majmu’ul fatawa.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »