An kafa jihar Kwara ne a ranar 27 ga watan Mayu shekarar alif 1967, lokacin da gwamnatin mulkin soja ta tarayya ta Janar Yakubu Gowon ta raba yankunan zuwa hudu da suka zama Tarayyar Najeriya zuwa jihohi 12. A lokacin da aka kirkiro jihar dai ta kunshi tsoffin lardunan Ilorin da Kabba na yankin Arewa a lokacin kuma da farko aka sanya mata suna jihar yamma ta tsakiya amma daga baya ta koma “Kwara”, sunan yankin kogin Neja.
Tun daga shekarar alif 1976 jihar Kwara ta ragu sosai a sakamakon kara yin atisayen samar da jihohi a Najeriya. A ranar 13 ga watan Fabrairun shekarar alif 1976, aka cire yankin Idah/Dekina na jihar tare da hadewa da wani bangare na jihar Benue/Plateau a wancan lokaci suka kafa jihar Benue.
A ranar 27 ga watan Agustan shekarar alif 1991, kananan hukumomi biyar, da suka hada da Oyi, Yagba, Okene, Okehi da Kogi, su ma an fitar da su a matsayin wani bangare na sabuwar jihar Kogi, yayin da ƙauyuka shida na karamar hukumar Borgu ta hade da jihar Neja. Manyan kananan hukumomi masu yawan jama’a sune Ilorin da Offa.
Jihar Kwara na da albarkatun ma’adinai masu yawa kamar su Tourmaline, Tantalite, da ma’adanai masu yawa a yankin arewa. Cocoa da Kolanut a Kudancin Oke – Ero, Ekiti da Isin LGA.
Jihar Kwara ta kunshi kananan hukumomi goma sha shida. Su ne kamar haka:
Asa, Baruten, Edu, Ekiti, Ifelodun, Ilorin Gabas, Ilorin South, Ilorin West, Irepodun, Isin, Kaiama, Moro, Offa, Oke Ero, Oyun, Patgi
A shekarar 2006, yawan mutanen Kwaran ya kai miliyan 2.37 bisa ƙidayar da aka gudanar a Najeriya a shekarar 2006.