Wasu Matsalolin Da Jinnul Aashiq Ke Haddasawa A Mahaifar Mace

0 518

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Duk da yake akwai wasu lalurorin da suke haddasa wasu daga cikin matsalolin mahaifar mace, amma a mafiya yawan lokuta jinnul Aashiq suna sanyawa mace irin su, musamman ma idan akaga matsalar ta yi yawa kuma ta ki ci ta ki cinyewa, ko anje asibiti an rasa gano matsalar. Ga kadan daga cikin matsalolin kamar haka:

1- Suna haddasa yawan barewar ciki.

2- Suna haddasa toshewar bututun da kwayoyin halitta ke wucewa ta wajansa (fallopian tube), kuma hakan yana sabbaba rashin haihuwa.

3- They make a clean woman feel a generation or smell from her body when she is menstruating or sometimes, or clean and puts on her turban.

4- Idan budurwa ce ko bazawara kuwa bayan sun sanya cututtukan da muka fadi a rubutun baya, sai kaga sun sanya mata rashin son aure ta yadda za ta rika kyamar duk wani wanda ya zo wajanta da maganar aure, ko kuma taji dazarar anzo mata da maganar aure sai dai taga lamarin ya rushe a rashin wani dalili, amma kuma sai kaga tana kula wasu wadanda ba auranta za suyi ba.

5- Suna sanya mace ta zauna ta rika sharar kuka da hawaye na rashin dalili haka kawai ba tare da an yi mata komai ba.

Da sauran su…

ME YAKE JAWO IRIN JINNUN NAN HAR SU SHIGA MAHAIFAR MACE ?

1- Yin sakaci ko yin wasa da dokokin ALLAH musmman ma rashin cika sallolin farilla 5.

2- Rashin karanta Alqur’ani ko sauraronsa,

3- Yawan Sauraron kade-kade da wake-wake.

4- Rashin yin Addu’a yayin saduwar aure.

5- Rashin yin Addu’a yayin shiga banɗaki (toilet) da lokacin da ake cire tufafi.

6- Rashin yin Addu’a yayin fara cin abinci, da lokacin kwanciya bacci.

7- Rashin yin Azkaar na safiya da maraice/yamma.

8- Yin Istimna’i ( masturbation) mace tayi ta yin wasa da al’aurarta har taji dadi ko makamantan haka.

9- Yin hulɗar auratayya tare da wasu mazan da ba mijinki ba, hakan ma yana iya sabbaba ALLAH ya azabtar da wacce ke yin haka da wannan lalaurar.

10- Sanya tufafin da suke bayyanar da wasu surorin jikin ki.

Wadan nan Kadan kenan daga cikinsu, Insha ALLAHu a rubutu nagaba za muji mafita da kuma yadda yakamata muyi domin samun kariyar ALLAH game da wannan lalaurar.

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.🤲🏻)

Domin karin bayani:
👇👇👇

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »