Wasu Alamu Dake Nuna HASSADA Tayi Tasiri A Jikin Yaro.

0 381

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Idan hassada tayi tasiri a jikin yaro za kaga yaron yana yin wasu abubuwa kamar haka:

1- Jikinsa yarika yawan daukar zafi a kansa da kirjinsa da kuma kafadarsa.

2- Jinkirin fara magana ko tafiya, sai kaga yaro har yakai wasu shekaru bai fara magana ko tafiya ba, ba tare da wani dalili na zahiri ko na likitanci ba.

3- Aji jikin yaro yana wani irin wari musamman a hammatarsa, kasan cibiyarsa da kuma hancinsa.

4- Yawan yin kuka cikin dare.

5- Yawan yin barcin da yake wuce qa’idar da ake bukata, wasu kuma su kasa yin barcin.

6- Halittarsa ta rika sauyawa haka kurum ba tare da wani dalili na zahiri ba.

7- Yin kuka yayin da ake wanke masa fuska.

Sa sauransu…

MAFITA:

A samu ruwan sanyi na sama ko na rijiya gwargwadon wanda zai iya wanka da shi, sai a karanta Fatiha, Ayatul Kursiyyu, Ikhlas, Falaqi da Nasi ( sau adadin da za ku iya) a cikin ruwan a ba shi yasha sauran kuma ayi masa wanka da shi, amma a wuri mai tsafta da tsarki ba a bandaki ba.

Sai a samo LEMON TSAMI guda daya ( Kore, danye wanda bai nuna sosai ba), sai a yanka shi gida biyu, a dau yanka daya sai a rika gogawa yaron a kansa ana maimaita kiran sallah gwargwadon iko, sai a dau ragowar dayan kuma a rika goga masa a kirjinsa da cikinsa ana maimaita wannan Addu’ar yayin da ake gogawar: A’UZU BI KALIMAATILLAHI ATTAAMMAAT MIN KULLI SHAITAANIN WA HAMMAH WAMIN KULLI AININ LAAMAAH.” ( Sau adadi da dama).

A maimaita haka safe da yamma har tsawon kwanaki 3, da YARDAR ALLAH za kuga sauyi cikin HIKiMAR ALLAH Ubangijin kowa da komai.

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.🤲🏻)

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »