Takaitaccen Tarihin Jihar Yobe
A ranar 27 ga watan Agusta, shekarar alif 1991 gwamnatin Janar Ibrahim Babangida ta cire jihar Yobe daga jihar Borno. Aka kuma fitar da Babban birnin ta Damaturu. Jihar Yobe dake arewa maso gabashin Najeriya tana da fadin murabba’in kilomita 45,502.
Yobe tana iyaka da jihar Borno daga gabas, jihar Gombe a kudu, jihohin Bauchi da Jigawa a gabas da Jamhuriyar Nijar daga arewa. Yobe ta kasance daga cikin jahohi masu zafin gaske, sai dai a kudancin jihar da ke da yanayi mai kyau.
Kabilar Kanuri ce ke da rinjaye a jihar, kuma ta kasance misali na jurewar cibiyoyin siyasa na gargajiya a wasu yankunan Afirka. A can ne sarakunan tsohuwar Daular Kanem-Bornu suka taka rawa a siyasar wannan yanki kusan shekaru 1000.
Manyan kabilun da ke zaune a jihar Yobe sun haɗa da Kanuri, yayin da sauran kabilun suka hada da Ngizim, Karai-Karai, Bolewa, Bade, Hausa, Ngamo, Shuwa, Fulani (Bura), da kuma Maga.
TATTALIN ARZIƘIN JIHAR YOBE
An yi la’akari da sanin su da Noma, kamun Kifi da kiwo ke ba da aikin yi ga sama da kashi 80% na Al’ummar jihar.
Yayin da jihar Yobe jihar noma ce kuma tana da wadatattun wuraren kamun kifi da ma’adanai na gypsum, kaolin, da quartz. Kayayyakin da suka fi Nomawa a jihar sun hada da: Gyada, Wake, Auduga. An kuma ce jihar tana daya daga cikin masu manyan kasuwannin shanu a yammacin Afirka dake Potiskum.
ƘANANAN HUKUMOMI
Jihar Yobe tana da kananan hukumomi 17 Su ne kamar haka: Bade, Bursari, Damaturu, Geidam, Gujba, Gulani, Fika, Fune, Jakusko, Karasuwa, Machina, Nangere, Nguru, Potiskum, Tarmuwa, Yunusari, Yusufari