Amfanin Ciyawar Nonon Kurciya Ga Masu Fama Da Matsalolin Fata.

0 430

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Duk mai fama da wasu matsalolin fata Kamar haka:

1- Kurajen fata.
2- Kazuwa
3- Kyasfi
4- Kurajen fuska
5- Matsalar man shafawa ko sabulun wanka.
6- Skin infection.

Da sauran wasu matsalolin da suka shafi fatar mutum, to ga mafita nan da Yardar Allahu.

Abinda za ka nema kawai shi ne : Ciyawar nan mai suna NONON KURCIYA ana samunta a ko ina a fadin kasar nan, ka debota sai ka wanke ta ka tsaftace ta sosai, bayan haka kuma sai ka mistsiketa ko ka kirba ta sai ka matse ruwan ( Da ma ruwan kawai ake bukata).

Idan ka fitar da ruwanta, to shi ne za ka rika shafawa a kan fatarka safe da dare ka dau tsawon sati biyu kana yin haka, In sha ALLAH za kaga abin mamaki game da matsalar fatarka, lamarin kamar almara amma za kayi mamaki matukar gaske kuma sai ga godewa ALLAH domin shi ne ya warkar da kai…Domin za kaga ka rabu da matsalar da ke damunka a tsakanin lokacin da YARADR ALLAH.

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.🤲🏻)

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »