Assali Da Kuma Yadda Garin Gaya Ya Samo Asali

0 545

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Marigayi Maje Ahmad Gwangwazo ya kawo a littafinsa ‘Tarihin Kano kafin Jihadi’ cewa asalin garuruwan Kano, Gaya da Rano ya samu ne daga wasu mutane uku waɗanda suka yiwo balaguro tare da ahalin su daga ƙasar Habasha tare da ƴanuwansu Maguzawa.

Sunayen waɗannan mutane kuma jagororin tawagar sune Ranau, Gayya da Dala, kuma sun yiwo wannan balaguron ne tun kafin haihuwar Annabi Isa A.S. (shekaru sama da dubu biyu da suka gabata kenan).

A cewar marubucin, Ranau ne ya soma zama a garin Rano, kuma daga gareshi aka samar da sunan Rano, Dala ne ya soma zama akan dutsen Dala na kano, kuma daga gareshi aka samar da sunan dutsen Dala, haka kuma Gayya ne ya soma zama a inda garin Gaya yake a yanzu kuma daga gareshi aka samar da sunan Garin Gaya.

Masana irin su marigayi Alh Maitama Sule Ɗanmasanin kano da wasun sa duk sun haɗu akan cewa tabbas asalin (Hausawa) mutanen Gaya daga Habasha suke, kuma shi kansa wani shahararren mutum wanda aka ce daga sunan sa aka samo sunan garin Kano mai suna ‘Kano maƙeri’, daga garin Gaya yake. Har ma sun ƙara da cewa Bagauda wanda tarihi ya kiyaye a matsayin sarkin Kano na farko shima ɗan garin Gaya ne.

Amma a wasu zantukan na tarihi musamman waɗanda suka fito daga garin Gaya, an samo wani abu mabanbanci da wannan game da asalin kafuwar Gaya.

Tarihin ya tafi akan cewa zamani mai tsawo da ya gabata, inda garin Gaya yake a yanzu jeji ne mai cike da albarkatun namun daji.

Akan haka wani mafarauci da ake kira da suna Bagauda tare da ɗanuwan sa mai suna Gayya, suka ruski wajen tare da zama a inda garin Gaya yake a yanzu. Bagauda ya kafa rumfar sa a wani waje da har zuwa yanzu ake kira da suna ‘unguwar Bagauda’. Ya zama nan ne makwancin sa, a kullum ya kan shiga daji yayi farautar namun daji sannan ya dawo rumfar sa ya sarrafa.

Sannu a hankali sai mutane musamman ƴanuwan sa mafarauta suka fara riskar wajen tare da kafa rumfunan su na kwana. Kwanci tashi albarka na ƙaruwa, mutane na ƙara kwarorowa, daga mafarauta zuwa manoma, zuwa maƙera, zuwa matafiya masu shigewa zuwa Borno, da dai sauran masu sana’o’i daban-daban. Wannan kuma shine asalin yadda aka kafa garin Gaya.

Game da yadda aka samo wannan suna na Gaya, an samu zantuka guda biyu.

Na farko an faɗa cewa jim kaɗan da soma kafuwar garin Gaya a wancan lokaci, sai Bagauda ya ɗaura niyya tare da barin garin. Daga nan yayi yamma yana tafiya cikin dazuka gaminda farautar namun daji a hanya. Akan haka ya je ya sari wani gari da ake kira ƴar Gaya, sannan kuma da ya ƙara tashi, bai sauka ba sai a inda garin kano ya ke a yanzu. A wancan lokacin ne ya sari kano.

Littafin tarihin kafuwar kano kuwa ‘kano chronicle’ ya sanya cewar Bagauda shine sarkin kano na farko, kuma ya soma mulki ne a shekara ta 999 A.D.

Wanda Bagauda ya bari a Gaya shine ɗan uwansa Gayya wanda suka riski wajen tare, don haka shine ya zamo jagoran mutanen da suka cigaba da zama a wurin, kuma daga sunan sa ‘Gaya’ ta samo asali.

Zance na biyu kuwa ya tafi akan cewa sunan Gaya ya samo asali ne daga wani jagora da aka taɓa yi a farko-farkon garin (ko Gayya ko kuma sarki na farko mai suna Sarki Kwalo).

Ance wannan jagora yana da kyauta da haba-haba da mutane. Ya kasance duk baƙon da ya isa gareshi sai ya samu wani abu na alheri yayi masa.

Akan haka ya kasance idan wasu suka ziyarce shi alhali ya gama rabar da abubuwan da yake dasu ga masu ziyartar sa, maimakon ya barsu haka nan ba tare da ya basu komai ba sai yace ” sai hakuri, babu abinci, babu nono, sai dai gaya”.

Sai ya ɗauko gayan ya bayar.

Don haka sai mutane ke kiran sa da suna ‘mai gaya’. Kuma daga gare shi sunan Gaya ta samo asali…

Marubuci:

Sadiq Tukur Gwarzo

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »