Hanyoyin Kariya Da Magance Kodewar Fata.

0 323

Lokuta da yawa fata kan kode ne saboda shiga cikin rana ko kuma amfani da wasu mayuka wanda fatar ka bata karbesu ba, wasu lokutan ma harda wasu abinci da mukanci na yau da kullum.

Hakan tasa mukazabo muku wasu muhimman magumguna wanda zai kare fatarka daga wannan kodewar. Idan kuma tuni fatar taka ta kode to wannan zai baku damar fatar taku ta dawo normal insha Allah.

KOREN GANYEN SHAYI:

Green tea

Zaku tafasa koren ganyen shayi hade da na’ana. Bayan kun tafasa sannan a bari hadin ya jiku kamar na tsawon sa’a daya sannan a sanya a gidan sanyi, sannan a wanke fuskar da hadin ko kuma a samu auduga ana shafawa a inda fatar fuskar ta kode.

RUWAN DANKALIN TURAWA:

Zaku samu dankalin turawan ku a fereye shi sannan a wanke sai a matse ruwan sannan a rika shafawa a fuska musamman inda fatar ta kode. hakan zai magance matsalar fatar sannan kuma yana kareta daga sake aukuwar hakan.

MADARA:

Zaku samu Madara mai kyau a sanya a freezer har sai ta yi sanyi sosai sannan a samu tawul karami a rika tsomawa ana goge fuskar da shi. Madara na sanya hasken fata sannan kuma tana warkar da wannan kodewar fatar.

GURJI:

Zaku nemi Gurji sannan a yanka sannan a sanya a gidan sanyi har sai ya yi kankara sannan a rika shafawa a wannan wajen da fatar ta kode ko kuma a rika daurawa wurin har sai ya narke.

GANYEN ALOE BERA:

Zaku samu wannan ganye na Aloe bera sai a matse ruwan da ke ciki a rika shafawa a fuskar a kullum har sai kodewar ta yi sauki. Wannan ganye na da matukar mahimmanci a fata, don haka yana da kyau ake shuka Aloe Bera a gida.

RUWAN TUFFA:

Shima wannan hadinsa kusan daya ne dana Dankalin Turawa zaku iya samun wannan ruwan ne bayan an kankare sannan a matse. Sai a rika shafawa a fuska har sai ya bushe. Haka za a rika yi a kullum.

RUWA:

Yawan shan ruwa sosai ga mai dauke da wannan matsalar ta kodewar fata, sannan za a iya sanya ruwan ya yi kankara sannan a rika shafa wannan kankarar a inda fatar ta kode.

ABIN LURA:

Wannan magunguna da muka lissafo a sama bawai gabadaya zakuyi amfani dashi lokaci guda ba, zaku zabi daya ne wanda kukaga yafi muku sauki sai kuyi amfani dashi.

Kuma kunsan magani karba karba ne idan ka gwada wani bai maku ba saiku gwada wani, hikimar kawowa da yawa kenan. Allah yabada saa.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »