Yadda Zaki Hada Tamarind Juice.

2 910

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Yar uwa nasan cewa kinsan tamarin juice iri daban daban, haka zalika wannan ma da zamu kawo muku yanada matukar dadi in har kinyishi yadda ake bukata.

Kawai abinda zaki bukata shine:

 • Tsamiya (Tamarin).
 • Suger.
 • Citta.
 • Kanumfari.
 • Tiara (Idan Ana Bukata).

Yar Uwa sai Kuma Yadda Zaki Hada wadannan abubuwa su baki Juice Mai Dadin Gaske.

TSAMIYA: Yar uwa da farko zaki samu Tsamiyarki (Tamarin) mai kyau yadda ake bukata Saiki kawo ruwa ki zuba a cikinta saiki bata lokaci mai tsawo don ta gama narkewa.

Kokuma bayan kinsamu tsamiyar taki saiki dafata sosai saiki tace ruwan a ajiye a gefe.

KANUMFARI DA CITTA dinki saiki Jukasu a cikin ruwa madai-daici suma su juku sosai saiki tace ki ajiye a gefe.

SUGER: Saiki samu sukarinki yadda ya dace sai a sanyashi a tukunya yadan fara narkewa da kansa kada a bari ya kone sai ki sauke shi.

Zaki kawo wannan ruwan tsamiya da kika tace saiki zuba akan wannan dafafen sukari naki saiki juyashi sosai. Saikuma ki dauki ruwan Kanumfari da Citta dinki da kika tace shima saiki zuba akan ruwan Tsamiya da Suger naki.

Zaki juya sosai sai kuma ki kawo TIARA dinki bamai yawa ba saiki zubata a ciki ki kuma juyawa.

Yaruwa shikenan angama saiki sanyashi a Freezer yayi sanyi ki bawa mai gida da yaran gida su sha.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

 1. Tom Michalowsky says

  I’m getting a touch difficulty I actually are not able to appear to be in a position to signed up your current feed, I’m making use of yahoo and google readers.

 2. Aisha musa says

  I really i like cooking but am not gud in it, thank a lot for ur sports at inter net

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »