Yadda Zaku Hada Fruit Juice

1 741

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Fruit Juice, juice ne mai dan Karan dadi Wanda in har kin hadashi yadda yakamata kika bawa mai gidanki kokuma Wanda zai zama mai gidanki (Saurayinki) kenan to Ina tabbatar Miki saikin tare bayansa Don karya Fadi saboda dadinsa musanman idan yayi sanyi sosai.

ABIN BUKATA:

Mangoro 🥭

Ayaba 🍌

Gwanda

Lemo 🍊

Sukari

Madara

YADDA ZAKIYI HADIN:

Yar uwa da farko Zaki samu lemonki ki bareshi saiki tace ruwansa ki ajiye a gefe guda.

Saiki kawo Mangoro 🥭, Gwanda da Kuma ayaba 🍌 dinki saiki baresu sosai bayan kin bare bawan nasu, Saiki samu abin nikawa Kamar blender dinki saiki zubasu a ciki.

Saiki nikasu sosai bayan kin tabbatar ya niku saiki kawo ruwan wannan lemon saiki zuba, kikawo Madara maidan yawa saki zubata saikuma sukarinki yadda ya kamata Shima kizoba a ciki saiki Kuma markadawa.

Masha Allah shikenan ya gamu Sai Sha kawai yaruwa idan har yayi yadda akeso to zaa ganshi yayi fari to zaiyi test mai kyau.

ABIN LURA:

Idan a take Zaku sha saiku samu kankara a nuka da ita, idan Kuma baa lokacin zaa shaba saiku saka a freezer Don yayi sanyi.
Get real time updates directly on you device, subscribe now.

  1. Tom Michalowsky says

    Hello! Just dropped by to write great website. Keep up the good work youre doing!

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »