YADDA AKE GYARAN JIKI (FATA) TAYI LAUSHI KUMA TAYI KYAU

0 3,265

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Yadda Ake Gyaran Jiki Yai Laushi Kuma Yai Kyau: Gyaran jiki ya na taimakawa Namiji ko Mace ta dade ta na more jikinta. Fatar mutum ta zama lafiyayya Kuma abin sha’awa. Shine za ka ga Mace Komai yawan shekarunta, haka komai yawan haihuwarta. Ta na da kyakkyawan jiki.
Gyaran jiki ya samo asali ne daga wajen Larabawa. Sai Barebari wato daga mai duguri anan kasar Najeriya. Hakama Turawa sun yi mayuka kala-kala domin gyara fata.
Sai dai duk Sanda mutum ya ke so zai dinga gyara jiki . To ya zama tilas ya kula da mafi muhimmanci, wato ya bi matakai gyara jiki.


MATAKAI GYARAN JIKI:
1 – Cin lafiyyen abinci.
2 – Yawan Shan ruwa .
3 – Yawan Cin ‘ya’yan itatuwa.
4 – Atisaye ( motsa jiki) .
5 – Amfani da kayan gyaran jiki ( Dilka).


GYARAN JIKI NA DILKA:


Za’a zuba Dilka a cikin mazubi. Sai a zuba masa ruwan zafi. Bayan jimawa sai a zuba kurkum, da mai zaitun , da kwai .
Sai a kara ruwa dan dai-dai . Ashafe dukkan jiki har fuska. Idan ya bushe sai a murje jiki da shi.


GYARAN JIKI NA ALKAMA:


Za a nika Alkama ne, a tankadeta tai lukwui. Sai a soyata kamar yadda ake idan za’a yi kunun alkama.
Za’a zubawa soyayyiyar alkama yis. A zuba ruwa a kwabata. A shafe duk jiki da ita. Bayan dan lokaci sai adinga murje jiki ko ina.


GYARAN JIKI NA KHALDA ( OATS):


Za a zubawa khalda (Oats) madara. Sai kuma a matsa lemon tsami kadan. A juyashi a kwaba sosai. Sai ashafam but shi duk jiki. Bayan dan lokaci sai amurje duk jiki.
A karshe lalle akwai bukatar mu dinga waiwayar gyaran jikinmu duk sati in da hali. Ko kuma duk Wata. Ya danganta da yadda ake da hali, lokaci da himma.
Duba yadda ake ado da kwalliya ta Musamman.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »