ABUBUWAN HADAWA
- Kan-kana
- Abarba
- Sugar
- Flavour
- Kan-kara (Ice Block) optional
YADDA AKE HADAWA
Da farko za ki cire yayan kan-kana sai ki sa a blender ki gyara abarba itama ki sa sai ki sa kan-kara (Ice block) ki yi blending na su baki daya.
Idan ya yi sai ki tace ki sa sugar da flavour, amma kuma zaki iya sanya sugar da flavor dinki a ciki gabadaya saikiyi blending dinsu baki daya. Yafi sauki kuma yafi dadi.
ABIN LURA:
Zaki iya sanya shi a freezer yayi sanyi idan baki samu kan-kara (ice block) a lokacin hadawa ba.
BANBANCIN TSAKANIN JUICE DA SMOOTHIE DA KUMA MILKSHAKE.
SMOOTHIE:
Idan ki ka yi blending wannan kayan marmari (fruits) kawai har sai daya niku sosai ki sa kankara, to wannan SMOOTHIE ne.
JUICE:
Idan kuma, bayan nikan, ki ka tace shi, to wannan JUICE ne.
MILKSHAKE:
Idan kuma ki ka nika ki ka sa ruwa da madara wanann MILKSHAKE ke nan.
Dafatan An Fahimci rabe-raben su Uwar Gida.
A sha Ruwa lafiya.
Aslm gsky muna gdy Allah yakara basira Allah yasaka da alkhari
Amin Thuma Amin.