HAIHUWAR SA.
An haifi Aminu Ladan Abubukar wanda aka fi sani da (Alan waka), a shekarar alib 1974 a unguwar Yakasai cikin birnin kano.
KARATUN SA.
Aminu Ala ya fara karatunsa na Firamare a tudun Murtala Primary School daga 1980 zuwa 1986 daga nan ya wuce Makarantar Sakandire dake Dakata kawaji daga 1986-1992.
Aminu Ala ya samu tsaiko a karatunsa wanda hakan ne ya bashi damar shiga harkar rubutun kirkira wanda daga baya kuma ya shiga harkar waka gadan-gadan inda har takai yana da kamfanin Waka mai suna TASKAR ALA GLOBAL.
FARA WAKA DA RUBUTU
Amunu Ala ya fara waka ne tun a matakin Makarantar Islamiya da wuraren Maulidi, sai dai a cewar mawakin yace wakar tasa bata shiga cikin Alumma ba sai kusan shekarar 2003 ta Kafar sadarwar gidan Rediyon Jihar Kano. Sannan ya fara rubutu ne a shakarar alib 1992, rubutun nasa ya fara fita ne kuma a shekarar alib 1999.
raina fansa ne ga Annabi Babba dan Babba da kuma wata wakar mai suna Mai duka sa in je madina
DAUKAKAR SA GA JAMA’A
Mafiya yawan wakokin Aminu Ala sun shafi al’umma ne da fadakarwa akan siyasa da zamatakewa wanda hakan ne ya bashi damar samun daukaka a wurin Jamaa harma da yan uwansa Mawaka.
LAMBOBIN YABO
Aminu Ala yasamu lambar yabonsa ta farko a wurin Marigayi Dr. Ado Bayero ya yin cika shekar arba’in da biyar akan mulki sai kuma karramawar daya samu a jami’o’i irinsu B.U.K da kuma Danfodiyo inda suka bashi jakadan Hausa sai kuma Jami’ar A.B.U da kwaleji.