Tarihin Makaman Kano Alh. Abdullahi Sarki Ibrahim Kashi Na 2

0 389

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Makama Abdullahi Sarki Ibrahim

Abdullahi Sarki shi ne dan Makama Ibrahim Cigari dan Makama Dahiru dan Makama Hamza dan Makama lsa I dan Makama Sa’idu dan Makama Umaru uban Jobawa.

Sarkin Kano Dr. Ado Bayero ne ya nada Abdullahi Sarki Makaman Kano ranar 19 ga watan Fabrairu, 1993 inda ya gaji mahaifinsa Makaman Kano lbrahim Cigari.

Kafin Malam Abdullahi Sarki Ibrahim ya zama Makaman Kano sai da ya rike mukamin magatakarda wato babban sakatare a ofishin shugaban kasa, Marigayi Janar Sani Abacha.

A bisa hakika, Wudil ta smi babban da, mai halayen iyayensa da kuma kakanninsa na rikon nulki da mutane.

Makama Abdullahi kwararre ne wajen jagorancin mulki, sai dai a kwaiwaye shi, ba za a fi shi ba. Mutum ne kuma wanda yake da fahimta la kwarewa da dagewa a kan mulki, ga shi kuma yana da ilimi da sanin dabarun zaman duniya.

A matsayinsa na mai sarauta, ya iya mulkinsa, yana zaune lafiya da dagatansa da masu unguwannin. Yana zaune tare da su zama na lafiya da nutsuwa, kuma talakawansa suna son sa matuka, suna nuna masa kauna da biyayya armar dai yadda suka yi wa mahaifinsa. Haka kuma mutum ne mai baiwa, yana yi wa mutanensa kyaututtuka.

Ya dai nuna kukarinsa a sarari na rike mutuncin mutanen Wudil, wannan ne ya taimake shi wurin jama’a yake samun yabo a wurin talakwwansa.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »