Yadda Ake Gudanar Da Sanaar Kuli Kuli

1 425

KULI KULI

Sana’ar kuli-kuli, sana’a dadiyar sana’a ce a gurin hausawa da ake sarrafa gyada don gudanar da ita. Masana sun bada. 

Kuli Kuli shine asarrafa gayda zuwa tunkuza sanan sai a soya ta, sai tabada Kuli-kuli. Kalmar Kuli-kuli tasamo asalin ne daga Kuli. 

Haka zalika kuli kuli ana iya cinsa ta hanyoyi da dama wasu sukan sanya shi acikin gari su sha wasu kuma sukan iya cinsa da mazar-kwaila wasu kuma suna cinsa haka zallansa. 

Kuli-Kuli nada sunaye daban daban kamar haka: 

  • Bakuru
  • Karago, da sauransu.

KAYAN AIKIN KULI-KULI 

Akwai kayan da ake amfnai da su wajen aiwatar da sana’ar kuli-kuli, su ne kamar:

Gyada:- Gyada ita ce babbar jarin gudanar da sana’ar kuli-kuli. Ita ake sarrafawa don yin kuli kuli.

Turmi da tabarya:- Ana amfani da turmi da tabarya wajen motsa nikakiyar gyada da aka mayar da ita tunkuza don fitar da mai da ke jikinta.

Dutse:- Ana amfani da dutse wajen matsar tunkuza don fitar da man gyada.

Faranti Ko Faifai:- Ana amfani da faranti ko faifai don ajiye mumullaliyar tunkuza don zubawa a kasko ko kwanon tuya.

Matsami:- Matsami shi ne abin da ake kwashe kuli-kulin da aka suya.

Kwanon tuya ko kasko: Ana amfnai da kwanon tuya ko kasko don tuya.

Matsani:- Matsani wani kwano ne da aka huhuda shi, ya zama kamar rariya. A cikinsa ne ake zuba kulin da aka kwaso daga cikin mai don ya karasa tsanewa. 

  1. MIRELES1555 says

    Thank you!!1

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »