Sana’ar Kiwo A Ƙasar Hausa

0 300

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Kiwo

Gabatarwa
Kiwo na ɗaya daga cikin sana’o’in ƙasar Hausa na dauri. Sana’a ce da ake gudanar da ita kamawa tun daga cikin gidaje har ya zuwa ruga da Fulani makiyaya kan yi. Babu wani gida da ba a kiwo a ƙasar Hausa (Alhassan, Musa, da Zarruƙ, 1982), sannan sana’a ce da ba gadonta ake yi ba (Zarruƙ, Kafin-Hausa, da Al-hassan, 1987).
Ana kiwata dabbobi ko tsuntsaye a gida ta hanyar ciyar da su da sauran abincin da aka ci aka rage ko kuma samar musu da nasu abincin daga kayan gona da dusar abinci. Idan kuma tsuntsaye ne kamar irin su kaji, agwagi, tantabaru, talo-talo, da sauransu, akan sake su suna kewayawa a cikin gida da wajen gida kamar gidan maƙwabta ko kwararo suna tsintar abincin da ya zube a ƙasa. Sannan kuma sukan je gurin zubar da shara kamar juji su tono ƙwari da dangoginsu a haka suke rayuwa. Idan sun hayayyafa zuwa wani lokaci, idan wata buƙata ta taso sai a kama a kai kasuwa dan samun abubuwan masarufi.

Ana kiwata abubuwan da suka shafi dabbobi kamar shanu, raƙuma dawaki, jakuna, tumaki, da awaki. Hakan nan ta fannin tsuntsaye ana kiwata kaji, zabi, talo-talo, tantabaru, da sauran su.

Idan dabbobi suka yawaita suka kai wani adadi, to sun zama garke kenan.
Sannan akan ware wani guri a cikin gida da ake ɗaure dabbobin a jikin itace, wannan itace na ɗaure dabbobi shi ake kira turke.

Amfanin Kiwo

Kiwo na da tarin amfani a ƙasar Hausa manya-manya daga ciki akwai:

  1. Samar da abinci: Kiwo na ɗaya daga cikin hanyoyin samar da abinci. Dabbobi kamar shanu da sauransu sukan samar da nono da ake amfani da shi kai tsaye a matsayin abinci. Hakan nan su kansu abubuwan kiwon abinci ne kai tsaye. Sau da yawa a irin gidajen da ake kiwon nama bai cika yanke musu ba, saboda akan samu kodai kaji ko ƙwansu, ko kuma tattabaru ana yankawa.
  2. Haɓɓaka tattalin arziƙi: Kiwo na ɗaya daga cikin hanyoyin samu kuɗi a ƙasar Hausa. Idan ƙaramar buƙata ta taso, akan kama ƙananan kiwo kamar kaji a kai kasuwa nan take a samu kuɗi. Babbar buƙata kuma akan kai dabbobi. Sannan kiwo shi ne tushen sana’o’in jima da
    fawa . Kenan muna iya cewa sana’ar kiwo tana da ‘ya’ya da suka haɗa da fawa da jima, da kuma jika wato dukanci kenan.
  3. Inganta harkar noma . A fannin noma dabbobi sukan yi abubuwa guda biyu; sukan zama hanyar samar da taki ga amfanin gona, sannan kuma ana amfani da su wajen yin noman.
  4. Sufuri: Haka nan kiwo na taimakawa wajen harkar sufuri.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »