Takaitaccen Tarihin Mace Ta Farko Da Tafara Tuka Mota A Najeriya

0 189

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Funmilayo Ransom Kuti (Matar Da ta fara tuka mota a Najeriya)

Funmilayo Ransom Kuti ta kasance mace daya tilo a jerin sunayen ‘yan gwagwarmayar neman ‘yancin kan Nijeriya. Fumilayo ta kasance malamar makaranta, ‘yar siyasa, mai fafutukar kare ‘yancin mata sannan kuma mai rike da sarautar gargajiya. Ita ce mahaifiya ga shahararren mawakin nan na Nijeriya, Femi Kuti. Funmilayo ce mace ta farko da ta fara tuka mota a Nijeriya. An zabe ta a majalisar sarakunan gargajiya, inda ta kasance wata wakiliya ta al’ummar Yarabawa. Fafutukar da ta yi ta janyo wa ‘ya’yanta bakin jini musamman lokacin gwamnatocin soji.

Cif Fummilayo Ransome-Kuti: (Mahaifiyar Fela Kuti) Abubuwa 11 da ya kamata ku sani game da mace ta farko da ta tuka mota a Najeriya

1, Cif Funmilayo Ransome-Kuti, mace ta farko da ta fara tuka mota a Najeriya, malama ce, mai fafutukar siyasa, mai fafutukar kare hakkin mata kuma mai fada a ji a Najeriya.

2, Ta kasance mai Tafiye-tafiye mai hazaka. Ta yi balaguro zuwa ƙasashe da yawa a duniya.

3, Kafin Najeriya ta samu ‘yancin kai – musamman lokacin yakin cacar baka (Cold War) ta yi tafiya zuwa tsohuwar USSR, Hungary da China, inda ta hadu da Mao Zedong – dan juyin juya halin gurguzu.

4, Ziyarar da ta yi zuwa kasashen da ke yankin Gabas ya fusata gwamnatin Najeriya ta ‘yan mulkin mallaka, da kuma gwamnatocin Birtaniya da Amurka.

5, A shekarar 1956, gwamnati ba ta sabunta fasfo din ta ba, saboda an yi imanin cewa manufarta ita ce ta rinjayi ‘yan Nijeriya musamman mata da ra’ayoyi da manufofin gurguzu.

6, An kuma hana ta bizar Amurka saboda gwamnatin Amurka ta yi zargin cewa ita ‘yar gurguzu ce.

7, Ta kasance daya daga cikin wakilan da suka yi shawarwarin samun ‘yancin kan Najeriya da gwamnatin Birtaniya.

8, Ta kasance wadda ta lashe kyautar zaman lafiya ta Lenin. Gwamnatin Soviet ta na bada kyautar ga fitattun mutane, fitattun ‘yan gurguzu da magoya bayan Tarayyar Soviet waɗanda ba ‘yan Soviet ba.

9, A cikin Fabrairu 1978, an jefar da ita daga tagar wani bene mai hawa 3 (Jamhuriyar Kalakuta) mallakar ɗanta mawaƙi, Fela. Hakan ya faru ne lokacin da sojoji dubu suka mamaye ginin. Ta suma kuma daga baya ta mutu a ranar 13 ga Afrilu 1978, daga raunin da ta samu daga faɗowar.

10, Wani lokaci a cikin 2012, don a mutunta ta, ana ɗauki hotonta domin bugawa a kan takardar kuɗi na N5000. Daga baya gwamnatin Najeriya ta janye shawarar buga Sabon kudin N5000.

11, Bayan rasuwarta, dan nata Fela ya kai akwatin gawar ta zuwa Barrack Dodan – fadar mulkin Najeriya a wancan lokacin kuma hedkwatar koli na sojan Najeriya ya bar ta a bakin gate. Yayi hakan ne domin wulakanta gwamnatin mulkin soja da Obasanjo ya jagoranta saboda mamaye masa kadarori da yayi sanadiyyar mutuwar mahaifiyarsa. Wannan mamayewa ya zaburar da Fela wajen yin waka mai suna “Coffin for Head of State”.

Rubutawa:

Tarihi Da Al’adu

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »