Tarihin Kabilar Tiv (Tibi) A Najeriya

0 369

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Kabilar Tiv (Tibi) suna ɗaya daga cikin mafi kyawun ƙabilu na Isra’ila da suka yi ƙaura zuwa nahiyar Afirka.

Asalinsu Daga Kabilar Bantu ne na ƙasar Zulu, a Afirka ta Kudu, sun yi ƙaura zuwa Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango a Afirka ta Tsakiya, da kuma Najeriya a yammacin Afirka.

Daga yankin Kwararafa na Kongo-Zaire, sun yi ƙaura zuwa tsaunuka bakwai a yammacin Kamaru tsakanin shekara ta alif 1750 zuwa 1800, lokacin da dukan al’ummomin yankin Apa na Kwararafa suka shiga cikin tashin hankali.

Don haka ya yi wa ‘yan kabilar Tiv da ke isowa sauki, su yi ta fafatawa a cikin kasa har sai da suka isa gabar kogin Binuwai da Katsina-Ala, wanda hakan ya tilasta wa Idomawa, tashi zuwa yamma.

A shekara ta alif 1800, duk mutanen yankin da aka fi sani da Jihar Binuwai a yanzu sun isa yankin, kuma sun koyi zama tare da juna.

Tiv suna nan a jahohin Benue, Taraba, da jihar Nasarawa.

Hedikwatar gargajiya ta Tiv land ita ce Gboko a jihar Benue, a nan ne fadar Tor Tiv take.

Tor Tiv wanda aka fi sani da Begha U Tiv (Zakin mutanen Tiv) shine babban sarkin gargajiya na kabilar Tiv.

Tor Tiv na yanzu shine (HRM, Farfesa Ortese Iorzua James Ayatse.)

Al’ummar Tiv mazauna jihar Benue sun bazu a cikin kananan hukumomi goma sha hudu na jihar (14) Benue
Tufafin al’adun mutane na da ban mamaki kuma yayi fice kamar sauran kayan kabilun Najeriya.

Tufafin kabilar Tiv ana kiransa A’nger kuma yana da kalolo biyu farin Launi da baƙin Launi, Baƙin Launi yana nufin cewa mutanen Tiv sun samo asali ne a matsayin baƙar fata a Afirka, Farin launi yana nuna Aminci da Ƙauna.
Ta wannan hanyar launuka biyu suna wakiltar halin zebra a cikin daji.
Zebra yana daya daga cikin halittu masu zaman lafiya da taushi, baya haifar da wata illa.

Mutanen Tiv sun shahara saboda fasahar noma da kuma al’adun Gargajiya

Tarihi Da Al’adu

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »