Amfanin Ganyen Rogo Ga Lafiyar Jiki

0 716

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Mai fama da matsalar karancin Jini zai tsinko ganyen ne kamar guda 10 zuwa 15, sai ya tsaftace shi ko ya markade a blender ko ya mistsikeshi yadda dai za a samu ruwa daga jikin ganyen, sai a tace ruwan a zuba masa madarar ruwa misali madarar Peak Milk gwangwani daya a juye a ciki sai a baiwa mai fama da matsalar karancin jini CIKIN IKON ALLAH za kuga jinin ya dawo cikin kankanin lokaci DA YARDAR ALLAH.

Masu matsalar ƙarancin jinin sun jarraba kuma ana ganin fa’idar hakan cikin IKON ALLAH.

Mai fama da matsalar karancin ruwan nono ma za ta iya yin wannan hadin tana sha sau biyu a rana har na tsawon kwanaki uku. Kuma ta rika yin miyar ganyen Rogo tana ci da tuwo ko Apu (fufu) ko sakwara da makamantansu.

In Sha ALLAHu za taga abin mamaki domin cikin kananan lokaci ruwan nonon zaizo, kuma yana samar da ingantacce kuma wadataccen ruwan nono ga mai shayarwa cikin IKO DA YARDAR ALLAH.

Kuma mai ciki ma ta rika cin miyar Ganyen Rogo yana yakar cutar ANAEMIA Wacce mai ciki ke dauke da ita DA YARDAR ALLAH.

ALLAHu A’alam.

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »