Takaitaccen Tarihin Kabilar Korowai Dake Papua New Guinea.

0 380

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Kabilar Korowai ƙabila ce mai matuƙar ban sha’awa da aka gano a yan shekarun baya a wani yanki dake Papua sabuwar Guinea. Har zuwa shekarun alib 1970, ba’a taɓa samun wani cikakken bayni a Kansu ba tsakanin su da ƙasashen yammacin duniya. A takaice ma, masana kimiyya sun yi imanin cewa kabilar a tunanin su Babu wata halitta ta Mutane a doran kasa da yawuce su. Ga abin da ya kamata ku sani game da kabilar Korowai.

SUNA ZAUNE A CIKIN GIDAJE MASU TSAYIN ƘAFAFU 140
Ɗaya daga cikin abin mamakin wannan kabilar shine sukan gina babban gida a saman bishiya wanda ke da tsayin ƙafa 140 a cikin dazuzzuka. An gina gidan bishiyar kuma an sanya shi a kan tudu, waɗanda suka tsara don kare kansu daga ƙauyuka masu hamayya. Waɗannan sukan hawa gidajen ne da tsani wanda suka hada da itacen bishiya.

Hoto daga Andaman / Flickr

SUNYI IMANI BABU WATA HALITTA TA MUTANE IDAN BASU BA.
Kabilar Korowai sun yarda cewa mutanen daba su ba Aljanu ne. Ana tunanin cewa har zuwa shekarun 1970, ba su taɓa gane wani a duniya ya wanzu a wajen kabilarsu ba. Wasun su har yanzu ba su taba ganin farar fata ba a rayuwarsu ba.

RAHOTANNI SUN CE SUNA CIN NAMAN MUTANE
Papua dake sabuwar Guinea na daya daga cikin kasashen duniya da ba a boye ake cin naman mutane ba, kuma har zuwa kwanan nan. Kabilar Korowai tana daya daga cikin kabilun da aka sani na karshe a duniya da suka kasance masu cin naman mutane. Saboda imanin Korowai na duk wani mutum daba dan kabilar su ba to Aljani ne, ya wajaba a kashe su cinye Namansa.

KABILAR KOROWAI SUNYI IMANI DA TSAFI
Har tsafi yana taka muhimmiyar rawa a kabilar taKorowai. Yayin da Kiristoci na mishan ke zaune a yankin tun daga ƙarshen 1970s, kuma sun yi nasarar mayar da wasu Korowai zuwa Kiristanci, da yawa sun ƙi barin ra’ayinsu na na tsafi da cin naman Mutane.

SUNA AMFANI DA BAKA DA KIBAU DON KAI WA DABBOBI DA MUTANE HARI.
Ba tare da wani fasaha na yammacin duniya ko kayan aiki ba, ana yin farauta ne tare da baka da kibiya. Wadannan kayan aikin ba wai kawai ana amfani da su don farautar dabbobi ba, har ma da farautar wasu mutane, masu kutse daga mutane da ke hamayya da su ko kuma baki da ba sa so.

SUNA AURAR DA YARANSU MATA BAYAN GANIN JININ AL’ADA NA FARKO MAZA KUMA IDAN SUNA DA SHEKARU 20.
Yawancin matan kabilar Korowai ana aurar da su ne a lokacin samartaka, bayan sun fara jinin haila. Gida jansu na bishiyar yawanci yana ɗaukar mutane 15, wanda zai ƙunshi maigida, matarsa ​​ko matansa da duk ƴaƴan da basu yi aure ba. Da zarar mace ta yi aure, ana ganinta a matsayin balagagge kuma dole ne ta bar gidan iyali ta zauna da mijinta.

Hoto daga Gudkov Andrey / Flickr

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »