Bani Da Lafiya Kashi Na Tamanin Da Hudu.

0 561

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Ummu Labeeba dai lamarin ya burgeta Kuma ya bata mamaki matuƙa har take cewa: Ikon Allah kenan, wato Annabi ya yi gaskiya domin Allah yana bayar da kariyarSA ne ga wanda ya lizimci ambatonsa da neman kariyarSA kadai.

Maman Sultan dai jikinta yayi sanyi tayi shiru tana sauraron su batace komai ba.

Ummu Bareerah: Wato lamarin nan a bayyane yake wallahy, domin duk wanda ya dukufa yin Azkaar din nan na safiya da maraice da lokacin kwanciya bacci babu abinda zan iya cutar da shi sai dai wani ikon Allah kuma.

Ummu Labeeba: Wannan haka batun nan yake, haka Labeeba itama ko da yaushe cikin Azkaar din nan take, ko da ta manta to fa sai ta yi su daga baya.

Ummu Bareerah tace: Allah Sarki, ai yaran suna da kokari sosai Wallahy Ummu Labeeba, ai ina jin wannan Addu’ar suke karantawa domin ita ma Bareerah kullum da safe sai ta karanta wannan Addu’ar: “LA ILAHA ILLALLAHU WAHADAHU LAA SHARIKA LAHU LAHUL MULKU WALAHUL HAMDU WAHUWA ALA KULLI SHAI’IN QADEER.” da sauran Azkaar (Sau 100 kafin ta tashi daga inda tayi Sallar Asubahi).

Kuma sai ta karanta Alqur’ani ko da shafi 1 ne kuwa.

Sannan idan tazo kwanciya bacci ma tana karanta Ayatul Kursiyyu, sai ta haɗa hannuwanta biyu ta karanta Ikhlasi, Falaqi da Nasi sai ta shafe jikinta gaba daya, sau 3 take maimaitawa ma.

Ummu Labeeba: Masha Allah, ai nima ingaya miki exactly yadda Labeeba takeyi kenan, itama Addu’o’in nan takeyi domin ita har alwala ma takeyi kullum kafin ta kwanta bacci.

Ummu Bareerah: Ai hakan Annabi Sallallahu alaihi Wasallama ya tabbatar cewa duk wanda ya karanta hakan to babu abinda zai iya cutar da shi a wannan daren.

Maman Sultan: Kai Maasha ALLAH, gaskiya kun tarbiyyantar da yaranku tarbiyya mai kyau wacce Allah zai basu kariya kuma ya tsare su da tsarewarSA sannan za ta amfanesu da ku a nan gidan duniya da kuma lahira.

Ummu Labeeba: Allah sarki, Ai sai dai muce Alhamdulillah domin Allah ne kadai ke da ikon shiryar da duk wanda yaga dama, idan bai shiryar ba duk wa’azin da za ayi masa bazaiyi tasiri ba.

Ummu Bareerah: Kinga fa ya kamata mu karasa wurin nan don na ga malaman sun fara isowa.

Ummu Labeeba ta kalli Maman Sultan tace: Amma dai tare za muje da ke ko?

Maman Sultan kwarai kuwa ai yanzu kuma insha ALLAHu kafata-kafarku duk inda za ku ina tare da ku.

(Insha ALLAH za muji me yafaru a rubutu nagaba.)

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.🤲🏻)

Domin karin bayani:
👇👇👇

Dan uwanku:
Idris M Rismawy (Abu Nu’aym)

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »