Bani Da Lafiya Kashi Na Tamanin Da Uku (83)

0 496

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

“Duk wanda Allah ya shiryar shi ne shiryayye kuma babu wanda zai iya batar da shi, haka ma duk wanda Allah yabatar shi ne batacce kuma bazai taba samun mai shiryar da shi ba koma bayan ALLAH.”

Su Labeeba suna karasowa wurin da Ummansu suke ne sai suka tarar da Maman Sultan tana yiwa Ummominsu godiya tare da fatan Allah yasaka musu da AlkhairinSA.

Abin yai matukar basu mamaki sai Labeeba ta kalli Bareerah suna girgida kai cikin mamaki basu dai ce komai ba.

Sai Ummu Bareerah tace: Kuje ku jira mu a dakin taron insha ALLAHu mu ma muna nan tafe.

Su Bareerah suka yi gaba abinsu, sai Labeeba take cewa Bareerah: Wai yar uwa me kika fahimta ne game da abinda ke faruwa tsakanin su Umma da Maman Sultan ne a yanzu?

Bareerah: Toh, nima dai abin ya dauremin kai wallahy, amma dai insha ALLAH Alkhairi ne koma menene tunda na ga alamar Maman Sultan kamar ta sauko fa.

Bayan sun wuce ne sai Maman Sultan ta cewa su Ummu Labeeba: Da ma kunsan yaran nanne?

Ummu Bareerah: Ai yaranmu ne, kinga wmai Pink din Hijab din Labeeba ce diyar wannan ce, ita kuma wannan mai brown din Hijabi Bareerah ce itace diya ta.

Maman Sultan: Maasha ALLAH, wato gaskiya kunyi dacen nagartattun yara sosai, sai kuci gaba da yima Allah godiya, domin su ne suke hana kasuwanci na tafiya yadda yakamata a Makarantar nan, domin duk lokacin da na shirya zuwa wurin bokaye da wasu sai kiga sunje sun lalata lamarin.

Ummu Bareerah: Ikon Allah, hanaku zuwa sukeyi ne ko kuwa?

Maman Sultan: A’a ko kadan wallahy, kawai dai zuwa suke yi su rika samun mutanen suna fada musu babu kyau zuwa irin wuraren nan haramun ne kuma masu zuwa wuraren bokayen nan ko malaman tsubbu shiga bala’i kala-kala, kuma ga tashin hankali wani lokacin ma har Aljanun suna taba mutum.

Ummu Labeeba: Allah Sarki, lallaikam yara sunyi kokari, Allah yasaka musu da AlkhairinSA.

Maman Sultan: Wallahy kuwa, ni kuwa a lokacin babu wadanda na tsana a makarantar nan kamar su, kuma ba sai daya ba ba sau biyu ba na sa bokaye suyi min aiki a kansu suyi maganinsu su lalata musu rayuwa, amma abin ya ci tura bokayen sai cewa sukeyi: Yaran nan fa ba sa tabuwa gsky, saboda suna kullum sai sun karanta wasu abubuwa.

(Insha ALLAH za muji abinda su Labeeba ke karantawa da har idna anyi musu sihiri ba ya cinsu kuma Shedanun Aljanu ke tsoronsu).

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.🤲🏻)

Domin karin bayani:
👇👇👇

Dan uwanku:
Idris M Rismawy (Abu Nu’aym)

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »