Takaitaccen Tarihin Aisha Najamu Ta Izzar So

0 640

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Takaitaccen tarihin rayuwar Jarumar fina finan Hausa ta cikin shirin izzar so wato Aisha Najamu Wanda aka fi sani da hajiya Nafisa,,

Aisha najamu yar asalin Jahar Jigawa ce An haifeta a shekara ta Dubu Daya da Dari Tara da casa’in da bakwai (1997) izuwa yanzu tana da shekaru Ashirin da biyar 25 A duniya.

SHIGARTA MASANA’ANTAR KANNYWOOD
Ta fara fitowa ne cikin wakokin Hausa daga bisani ta fara fitowa acikin shirin fina-finai masu dogon zango irin su Izzar So, Wanda shine fim mai dogon zangon da ya haskaka tauraruwar a ciki da wajen Nigeria

Izuwa yanzu ta kwashe fiye da shekaru biyu ta na fitowa a acikin fina-finai dabam dabam a cikin masana’antar ta Kannywood.

TA TABA YIN AURE
Jarumar ta bayyana cewa ta taba yin aure sau daya har da yara wanda har yanzu jarumar tana burin Idan Allah ya kawo mata nagari zata sake yi.

Sannan jarumar ta taba fuskantar Kalu bale a lokacin da ta taya Al’ummar Musulmi murna da zagayowar haihuwar Sayyadina Ali sai Al’umma sukayi mata ca akan cewa ta zama “yar Shi’a a wancan lokacin abin da ya bata ma Jarumar rai a lokacin kenan Wanda batajin dadin furucin da al’umma sukayi akan ta ba.

Bugu da kari Jarumar ta kasance mace mai kamun kai acikin masana’antar ta kannywood Wanda Acewar Jarumar a hirar da akayi da ita a Gidan talabijin na BBC Hausa Nigeria tace bata taba fuskantar wani kalubale na wani ya nemi yin lalata da ita ba saboda ta tsare mutuncin ta kuma ta kasance mace mai ganin girman nagaba da ita cikin masana’antar kuma suna girmamata.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »