Bani Da Lafiya Kashi Na Tamanin Da Biyar

0 523

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Mutane da sauran malamai duk suka dawo aka fara kintse-kintsen ci gaba da Muhadar, su Labeeba kuma a gefe daya suna ta jiran iyayensu har yanzu basu shigo ba ga shi kuma za a fara, sai can Bareerah tace: Bari dai na leka su naga suna ina ne ma haka tukunna, kuma me yatsayar da su ne haka?

Tana lekawa ne sai kawai ta hango su tare da Maman Sultan sun tunkaro wajan Muhadarar, cikin sauri cike da mamaki da farin ciki Bareerah ta sami Labeeba take ce mata: Yar uwa Albishirinki….!

Labeeba: Lafiya kuwa yar uwa, naganki cikin walwala haka kamar wacce aka yiwa Albishiri din kujerar Hajji..

Bareerah: Ai wannan ma duk kusan kamar hakanne, domin su Umma ne nagansu tare da Maman Sultan za su shigo wurin Muhadarar nan, kema kinsan ai abin da banmamaki gsky.

Labeeba tayi farin ciki tare da godiya ga Allah Ubangijin kowa da komai tana cewa: Alhamdulillah, Allah muna kara gode maka abisa wannan nasara da su Umma sukayi.

Su Ummu Labeeba dai suka shigo suka zauna wuri guda tare da Maman Sultan.

Bayan kowa ya zauna ne sai aka cigaba da muhadarar daga inda aka tsaya, Malama tana cewa: ” A duk lokacin da mace mai ciki take karanta wadan nan Addu’o’in taba sha tana shafawa a cikinta kuma tana karantawa da suararon Alqur’ani mai girma to tabbas za ta sami kariya daga wajan Ubangijin kowa da komai shine ALLAH, shi ma jaririnta zai samu.

Malama taci gaba da cewa: Kuma da zarar an haifi jaririn abinda yakamata uwa ta farayi bayan an tsarkake yaron shi ne: Ta ɗauke shi tayi masa Addu’ar sanya Albarka da kuma nemar masa kariyar Allah yakare shi daga dukkanin sharrin halittunSA. Saboda Addu’ar uwa ga Danta karbabbiya ce ta Alkhairi ki ta sharri.

Kar ko kusa afara daukar jaririn hoto ana ɗorawa a social media tana nunawa duniya jaririn da ta haifa, wannan kuskure ne da yawancin mata da maza sukeyi, alhali kuma ba’ayi masa wata Addu’ar neman tsari ba, a hakane masu Kambun-baka za su iya shafar jaririn, Mayu za su iya kama jaririn, nasu Hassada, Sihiri, tsafi da sauransu duk za su iya taba jaririn saboda iyayensa basuyi masa Addu’ar neman tsari ba.

Sai dai ayita ganin jariri ya fara rikicewa, ya fara rashin lafiya iri-iri, ga yawan kuka na fitar hankali ko da yaushe jikinsa yarika daukar zafi, kuma a rasa gano abinda ke damunsa..

(Insha ALLAH za muji cigaban rubutun a rubutu nagaba.)

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.🤲🏻)

Domin karin bayani:
👇👇👇

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »