“Wasu iyayen su ne ke fara rushewa yaransu mata farin cikin gidan auren su tun kafin su aurar da su, wajan neman taimakon wani mahaluki akan ya hana ko ya tabbatar musu da abinda Allah ne kadai ke iya hanawa ko tabbatar da shi.”
Mai NAPEP yace: Kwarai kuwa yar uwa, ai kafin mukai wurin malamin sai uwar take sanar da yarinyar abinda za ta fadawa shi malamin wanda take bukata, wallahi a lokacin kamar nayi magana saboda na ga gatsalin nata ga Allah ne ya wuce yawa, amma dai nayi shiru.
Labeeba cikin mamaki take cewa: Ikon Allah, gaskiya wasu iyayen su ne silar gayyatowa yaransu shedanun aljanun da za su zo su takurawa rayuwar zamantakewar aurensu ko su hana su zaman auren a karshe su kaisu su baro ba Imani ba Amana.
Mai Napep: Ai baki san ma wani abu ba, ashe yarinyar tana da Aljanu kuma irin baqaqen nan ne.
Labeeba: Subhanallah ! Ai ka ga irinta ko !
Mai Napep: Sai da suka gama abinda suka je yi wurin malamin na dauko su, cikin hanyar dawowar mu ne sai naji yarinyar tana cewa:
“Umma, ni fa wallahy a wurin malamin nan sai da gabana yayita faduwa, har na dauka ma ko aljanu na ne za su tashi, domin yadda naga yayita kuramin idanuwa wallahy na firgita sosai, saboda kinsan dai idan aljanu na suka tashi lamarin ba dadi yakeyiwa kowa ba fa…
Kawai sai ji nayi uwar ta yi tsaki tace: Zancen banza…
Yarinyar taci gaba da cewa: Wai anya kuwa Umma zan iya aikata abinda malamin nan yace min kuwa, saboda ni duk hankalina ya ki kwanciya da shi?
Mai Napep yakara da cewa: Wai kinsan abinda Uwar tacewa yarinyar?
Labeeba tayi murmushi tace: Kai ko Ina kuwa zan sani, sai kace nice Allan misru.
Mai Napep: Wallahy cewa yarinyar tayi: Yoo ke ai ba ki da wayo, bakisan sharrin kishiya bane shi yasa kike fadin haka, yoo ni akan kishiya ai komai ma zan iya, ko da kuwa zan rasa komai nawa don dai naga nayi galaba akanta.
Labeeba tayi murmushi tace: Ikon Allah kenan, Allah yakara tsare mana imaninmu.
Mai Napep: Ameen ya Rabb, ai ni kuwa sai na saka musu baki nake cewa: Ai Hajiya tunda dai yarinyar nan ta nuna ba ta so, kuma ga matsalar Aljanun da take fama da ita saboda gudun kar lalurar ta zama 10 da 20 kawai inaga ki kyale ta, kuyi ta rokon Allah da neman maganin da shari’a ta amince da shi.
Ai fa nan matar nan ta kada baki take cemin: Kai Mallam, ba ruwanka cikin sha’anin nan, Ni za ka gayawa ALLAH ko ka rigani zuwa duniyar ne da za ka kama cewa menene da menene, kawai kama bakinka kayi shiru ba ruwanka da duk abinda zai faru, ni n’a sha alwashin ko menene zan rasa sai na ga na amsowa yarinyar maganin nan.
Labeeba: Subhanallah.. Allah yakara tsare mana imaninmu, kenan fa har imaninta za ta iya rasawa a yadda take fadi.
Mai Napep: Yoo tunda kikaji ta fadi haka ai har shi ma, domin duk wanda zai kade kafa yaje irin wuraren nan ai imaninsa akwai kura sai dai Addu’a kawai.
Labeeba: Lallaikam, ai rashin cikakken imani ne ke kai mutane wurin da za su rasa imaninsu gaba daya.
Akazo inda Labeeba za ta sauka, bayan ta sauka ne tana kan hanyarta ta zuwa gida sai ta tarar da Mahaifinta Abu Labeeba a kan hanya tare da wani Malami kuma mai taimakawa wajan bayar da magani mai suna Abu Ruwaiha, ita dai batasan shi ba.
(Insha ALLAHu za muji ci gaban lamarin a rubutu nagaba)
Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.
Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.
(Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.)
Domin Ƙarin Bayani Game Da Darrusan Marubucin.
+2348031542026
https://t.me/Rismawymedicine
rismawy86@gmail.com