Bani Da Lafiya Kashi Na Goma (10)

0 504

Labeeba: Lallaikam wannan ba ƙaramar izina bace ga sauran yan baya musmaman ma su wadanda ke kokarin biyewa Maman Sultan, take ta kaisu ta baro tunda ga yadda dai ta faru da wannan.

Bareerah: Wato nima na sha wahala akan lalurar nan tawa, babu yadda Maman Sultan batayi ba akan wai na je takaini wajan irin miyagun malaman nan, amma na daure na mika al’amari na ga ALLAH bata samu nasara akaina ba.

Labeeba: Allah Sarki, lallaikam Kinsha fama kuma kin dogara ga Allah ne shi yasa ma kikaga taimakonSA..

Bareerah: Ai ba ma nan ba kadai, sai da na jejje wajan masu magani na Islamic kala-kala, su ma sai yanzu sai ahankali wallahy, saboda yan damfara da makaryata har da matsafa ma sun shigo lamarin da sunan Islamic medicine, dole sai da taka-tsantsan wallahi.

Labeeba: Ai kam nima fa mamakin da nakeyi kenan, dole ne masu neman magunguna su rika yin taka-tsantsan saboda kar su fada hannun mushrikai ko kuraye masu fatar Akuya.

Bareerah: Wallahy sai da na kasance duk inda naji mai maganin islamic medicine a garin nan na Bangon Gabas sai na je wurinsa, hatta ma a social media da gidajen talabijin da na rediyo sai na san yadda akayi na same su na karbi maganin.

Labeeba: Lallaikam kina kokarin neman magani gaskiya yar uwa.

Bareerah: Ai ashe duk yadda nake yi din nan kuskure ne, saboda kowa naji yana bayar da magani sai na karba ba tare da na tantance wanene mutum ne shi ba kuma wanne irin magani ne zai bani, sai da na saurari wani malami a islamiyyar mu, yayi mana bayani gamsasshe ya bambanta mana tskanin masu maganin da ya kamata mu rika karbar maganinsu da kuma wadanda bai kamata ba.

Labeeba ta duba agogo taga har lokacin Sallah ya yi, sai tace: Subhanallah ! Yar uwa muje muyi sallah kar muyi asarar yinta a farkon lokacin ta, idan mun dawo sai muci gaba da tattaunawar saboda ci gaban rayuwar mu.

Bayan su Labeeba sunje masallacin aka idar da Sallah, sai akayi sanarwa a masallacin ana cewa:

“Anyi wata bakuwar malama mai suna Malama Hanaan kuma za ta fadakar da yan uwa mata ne akan wasu abubuwan da zai amfane su a rayuwarsu ta nan duniya da lahira.”

Labeeba tana jin haka sai ta waigo wajen Bareerah take cewa: Yar uwa ko dai za mu tsaya ne mu saurari wannan fadakarwar?

Bareerah tace: Ai kuwa dai… Saboda na san za mu fadaka kuma mu karu sosai, saboda na san malamar kuma ina jin bayananta a gidajen yada labarai da dama.

Malama Hanaan tayi fadakarwa akan Mata masu zuwa wurin neman magani ko ina ba tare da ranta cewa ba, wasu ma har wajan Mayu da bokaye suke zuwa da kuma masu zuwa wurin malaman tsubbu domin biyan buƙatar su ta duniya akan kishiyoyinsu ko kuma mallake miji da sauran su.

Malama ta yi karin bayani akan yan mata masu zuwa wajan bokaye domin su mallake samarinsu, ta nuna illar hakan da kuma abinda hakan ke haifarwa duk mai yin hakan fushin ALLAH da kuma tabewa duniya da lahira kuma ga shi mafarkin da ake fata yaki tabbata, sai dai ayi ta cin kudaden su ba gaira ba sabab.

Bayan da aka tashi ne kowa ya fito daga masallacin sai wasu acan gefe suka kafa wata daba suna cewa: Hmmm ni fa ba saurarar irin matan nan nakeyi ba fa, saboda sai su kashewa mutum gwiwa ya kasa tashi tsaye ya tsare kansa, saboda ai ko Allah ma ya ce: Ta shi in taimake ka, yoo kuma sai mutum ya zauna haka siddam ! A’a wallahi ba da ni ba.

Wata tace: Ai ingaya miki yadda naji ta kunnen hagun haka ta fita ta kunnen dama ko shiga kaina maganar batayi ba.

Labeebah kuwa tana jinsu sai murmushi tayi tana girgida kai tana cewa Bareerah: Ikon Allah, kinji abinda wasu ke cewa kuma yar uwa, Hmm, Allah ya kyauta.

Bareerah: Ai dama babu mai sukar gaskiya sai mara gaskiya, babu mai kushe nagarta sai lalatacce, sannan kuma babu makiyin shiriya sai batacce.

Labeeba: Tabbas kam, ALLAH ya kyauta kuma yasa mudace. Wato irin wadan nan matan su ne bokayen nan ke kaiwa su baro a karshe kuma su rasa madafa ba su ga tsuntsu ba su ga tarko.

Bareerah: Ai fa… Amma su har yanzu sun kasa ganewa, saboda sun gani ya faru da su wance da wance ga sakamakon ba kyau, maimakon su dau darasi da izina amma sai kara afkawa ciki suke. Allah yakara shiryar da mu da su hanya madaidaiciya.

Bayan an tashi daga makaranta ne, Labeeba ta hau a daidaita sahu (NAPEP) zuwa gida sai ta tarar da wasu mata uwa da diyarta a ciki, suka zama su uku kenan a cikin adaidatan.

Akazo wani wuri sai matan suka sauka yarage Labeeba ce ita kadai a ciki, suna cikin tafiya ne sai mai tuka NAPEP din yacewa Labeeba : Wato yar uwa gaskiya duniyar nan ta lalace sai ahankali wallahi, yanzu kinga waɗan nan uwace da diyarta fa.

Labeeba ta gyara zama tana sauraron abinda mai NAPEP din zaice, tace : Eh , ina jinka, me yafaru ne da su?

Yaci gaba da cewa: Tun dazu ne na dauke su nakaisu gidan wani malami neman magani, wai uwar ce take nemarwa yarinyar maganin mallake saurayinta, abin wallahi ba dadi.

Labeeba tayi mamaki tana cewa: Saurayi kuma ba ma miji ba ! Kai jama’a wai yaushe za mu iya zama lafiya ne?

(Insha ALLAHu a rubutu nagaba za muji ci gaban lamarin)

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.🤲🏻)

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »