Oluwatobiloba Ayomide da aka fi sani da Tobi Amusan an haife ta a ranar 23 ga watan Afrilu shekarar alif 1997 ƴar wasan tsere ce a Najeriya wanda ta ƙware a tseren mita 100, Ta zama zakara ta farko a duniya a Najeriya a gasar guje-guje da tsalle-tsalle a lokacin da ta lashe gasar ta duniya a shekarar 2022 a tseren mita 100, inda ta kafa sabon tarihi a duniya na gudun dakika 12.12 a wasan kusa da na karshe, sannan kuma ta samu maki 12.06 a wasan karshe da ta yi nasarar samun kyautar lambar zinare.
An haifi Tobi a Ijebu Ode, dake Jihar Ogun, Najeriya, ga Mista da Mrs. Amusan wadanda malaman makaranta ne. Tobi, kamar yadda ake kiranta, ita ce ƴa ta ƙarshe ga ’mahaifanta, Ta yi karatun Sakandare a Makarantar Lady of Apostles, Ijebu Ode, Jihar Ogun.
Tun tana karama, Amusan ta kasance kwararriya ƴar wasa. Ta samu lambar azurfa a Gasar Matasan Afirka ta 2013 a Warri. Ta kuma samu kyautar zinare a tseren mita 100 a gasar wasannin guje-guje da tsalle-tsalle ta Afirka a 2015 da aka gudanar a Addis Ababa. A shekarar 2015, ta fara buga gasar All-African Games tana da shekaru goma sha takwas, ta samu lambar zinare a tseren mita 100.
Tobi tayi wasan tsere sama da guda 20, kuma ta samu nasarar samun nasara a wasanni guda 9 daga ciki harda wanda ta samu nasara a shekarar 2022 idan samu kyautar kofin zinare ta duniya.