Bani Da Lafiya Kashi Na Talatin Da Hudu (34)

0 471

Nan take kawai Salaha ta mike za ta fice tana cewa: Hehehe ai ingaya miki ba za ku gane lamarin nan bane kawai, yanzu fa dole sai mutum ya tashi tsaye karki bari kanki yarika kullewa a irin yanayin nan Ummu Labeeba.

Ummu Labeeba tayi murmushi sai take cewa: Ai ingaya miki duk wanda bai san girman ALLAH ba kuma baisan matsayin ALLAH akan shi kadai ne ke da ikon komai da kowa ba, to ba shakka shi ne wanda kansa ya kulle kuma mai tafiyar da rayuwarsa a makance a karshe ya afka rami mai gaba dubu cike da duffai akan duffai.

Salaha dai lamarin yabata mamaki matuka saboda ganin yadda Ummu Labeeba ta sauya ra’ayinta lokaci guda, shi ne take cewa: Wai Ummu Labeeba yaushe kika zama haka ne, saboda na ga a baya sam ba kya yimin haka, hasali ma rungumar duk wani abinda nazo miki da shi kikeyi hannu bibbiyu.

Ummu Labeeba tayi murmushi take cewa: Allah Sarki, ai ni kam yanzu sai godiyar ALLAH da ya ba ni Abu Labeeba a matsayin mijina saboda ya seta min rayuwata daga gurbatacciyar hanya zuwa nagartacciya, ya sauyamin muggan tunanin da nake yiwa hukuncin Allah da matsayinSA yanzu na kara tabbatar da cewa Abinda ALLAH yace zai tabbata shi kadai ne kawai tabbatacce. Alhamdulillah.

Salaha dai kam taga lallaikam Ummu Labeeba da ta yi nisa kuma ba wani sauran bayani, sai tace : Ni dai na yi nan sai anjima.

ABIN LURA

Ko kadan kar ku kuskura kurika baiwa masu tallata muku bokaye damar baje kolinsu a gaban idanuwanku ko a cikin kunnuwanku saboda wasu lokutan kafin ku ankara sai suyi awon gaba da imaninku alhalin ku baku sani ba. ALLAH YAKARA TSARE MANA IMANINMU.”

Bayan da Ummu Arqam ta isa gida ne sai take labartawa Abu Arqam yadda sukayi da Ummu Labeeba sai yake cewa:

“Wato Ummu Arqam abinda nakeso ki fahimta anan shi ne: Kawai mu fawwalawa ALLAH lamarinSA saboda shi kadai ne da ikon bayar da haihuwar nan da muke ta fafutikar nema ko kuma ya hana, tunda dai mun kashe kudi akn magungunan nan har mun gaji.”

Ummu Arqam: Hmm ai dama kai Abu Arqam kullum idan nayi maka maganar nan sai ka rika nuna halin ko in kula, duk da cewa kuma neman maganin nan fa ba haramun bane.

Abu Arqam yayi murmushi yace: ALLAH ya huci zuciyar ki, shi yasa ba na ce miki a’a a duk lokacin da kika kawo shawarar wani magani, saboda na san idan da ace tun farko ne nake nuna miki irin haka na tabbata da tuni auren mu ya dade da mutuwa.”

Haka wasu ma’auratan suke azalzalar junansu akan matsalar haihuwa, har su rika kokarin rabuwa da juna, Wal iyadhu biLLAH, wannan sam ba tsarin Addini bane, domin daga mijin har matar duk babu mai ikon baiwa kansa haihuwa sai Allah ya ga dama.”

( Insha ALLAHu a rubutu magaba za muni ci gaban tattaunawar Ummu Arqam da Abu Arqam)

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.🤲🏻)

Domin karin bayani:

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »