Bani Da Lafiya Kashi Na Talatin Da Biyar (35)

0 531

Ummu Arqam dai tayi shiru, sai can itama take cewa: Baka fahimceni da kyau bane Abu Arqam, na san ka yi kokari matuka kuma kana kan yin kokarin akan wannan lamari, amma ina so ka fahimci cewa ba a gajiya da rokon Allah kuma ba’a gajiya da neman sababin samun waraka (indai har ta inganta), kuma kar mu kuskura mu yanke kauna daga samun Rahamar Allah.

Abu Arqam: Ai dama ba wai na nuna na gaji bane ko kuma yanke kaunar samun Rahamar Allah ba a’a ko kadan, kawai ina jiye mana ne kar muzo a garin neme-nemen magungunanmu muje mu afka hannun mushrikai su hallakar da mu a ƙarshe kuma muyi hannun riga da imaninmu.

Ummu Arqam tayi murmushi sai cewa tayi: ALLAH yaja kwana Ya Maigidana Abu Arqam kuma yayiwa rayuwa albarka, ai Insha ALLAHu idanuwanmu suna gani muna Addu’a kuma mun dogara ga ALLAH Ubangijinmu na san ba zai taba wulakantar da duk wanda ya jingina da SHI ba.

Abu Arqam ya amsa yana cewa: Aameen ya Hayyu Ya Qayyum. Insha ALLAHu nina idan nafita waje zan nemi shi Abu Labeeba sai mu kara tattauanawar da shi akan matsalar.

Fitar Abu Arqam ke da wuya sai ga kiran Ummu Labeeba nan a waya tana kiran Ummu Arqam.

Ummu Arqam ta daga wayar cikin murmushi, bayan sun gaisa ne sai Ummu Labeeba ke cewa: Yar uwa na san ranki ya baci dazun nan ga.e da abinda Salaha tace ko?

Ummu Arqam: A haba dai yar uwa ai na san irin mutanen nan ne sosai, domin na sha haduwa da irinsu, domin akwai wata fa da tace za ta kaini wajan wani mai bayar da irin maganin haihuwa, take kwarzanta shi da cewa: Ai shi saboda tsabar tabbacin da yake da shi ma har cewa mutum yake a sayi kayan jarirai tun yanzu da Ragon suna a ajiye.

Ummu Labeeba: Kai jama’a, ammafa mutanen nan akwai rainin hankali, wallahy idan mutum ba ya tuna Girman ALLAH a zuciyarsa, kuma ya kwallafawa rayuwarsa samun d’à ta ko yaya ne sai kiga shedan ya kwashe shi ya je ya aikata ko ma menene.

Ummu Arqam: Na’am ashe kin fahimta, ai shi yasa nima nayi maza nabar wurin domin Shedan zai iya
Kawata min zantukanta a karshe kuma sai kiga na kasance tare da ita, ALLAH yakara tsare mana imaninmu.

ABIN LURA

“Tabbas haka batun nan yake, matukar kikaji ana yin wani sabo ko ana ambatar shirka to kawai kibar wurin ko kuma kafin ki ankara sai dai ki

ga kin tsinci kanki a cikinsu ke ma kin zama su. ALLAH yakara tsare mana imaninmu.”

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.🤲🏻)

Domin karin bayani:

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »