Ali Banat hamshakin dan kasuwa ne dan kasar Australiya, daga baya mai ba da agajin jin kai, daga yankin Sydney na Greenacre kuma dan asalin Falasdinu. Ya mallaki kamfanin tsaro da lantarki kafin a gano cewa yana da cutar kansa a watan Oktoban 2015. Bayan an gano cutar kansa, ya ba da duk wani abu da yake da shi don ayyukan agaji.
Ali Banat ( An Haifeshi A Ranar 28 Nuwamba 1982 Ya Rasu A ranar 29 Mayu 2018) ɗan kasuwan Ostiraliya ne, wanda asalinsa Bafalasdine ne, daga baya kuma ya kasance mai ba da taimakon agaji, daga yankin Sydney na Greenacre kuma Dan asalin Falasɗinawa. Bayan da ya kamu da ciwon daji, ya bayar da dukan abin da yake da shi ga mãsu yin sadaka. Ya mallaki kamfanin tsaro da wutar lantarki kafin a Gano Yana da cutar kansa a watan Oktobar 2015.
Bayani daya samu daga likitoci ne ya sanyashi gaggawar kokarin kyautar da dukkan dukiyar dayake da ita, ta hanyar taimakawa mabukata musammam a yankin aftica.
Kafin bayyanar cutar dake damunsa Dan kwalisar matashi ne dake gudanar da rayuwar masu kudi kamar dai yadda wasu matasan keyi idan Suna da kudi, ya Mallaki Mota Ferrari Spider mai tsadar tsiya, wacce ba kowanne matashi bane ke iya mallakarta, yana da kayan sawa na alfarma, tare da agoguna masu tsadar gaske, kusan dukkan abubuwan da Ali ke amfani dasu suna da daraja, amma cikin rahamar Ubangiji sai ya nufeshi da bin hanyar temakawa mabukata da dukiyarsa.
Ali yakan yawaita ziyartar Makabarta a kowanne lokaci, don hakan ya kara tunasar dashi lokacin zuwansa cikin kabari yana gaf da zuwa.
“Wallahi abin duniya duk ya fita daga raina, idan har aka sanar da kai cewa kwanakinka ragaggu ne, to duk wadannan abubuwan ba za ka yi tunaninsu ba,” inji Ali
A Oktobar 2015 ne ya kafa wata kungiyar Musulman duniya ‘Muslims Around The World Project” da nufin tallafawa marasa galihu musamman a kasar Togo inda suka samarwa mata 200 da suka rasa mazajensu gidajen zama kyauta. Suka kuma gina masallaci da makarantar marayu da karamin asibiti da sauransu.
Na kafa wannan kungiyar ne bayan da na gane cewa babu abin da mutum zai tafi da shi lahira face ayyukansa, duk dukiyar da ka mallaka duk a duniya za ka barta”. “In ji Ali Banat.
Bayan gano cutar, ya kafa ƙungiyar agaji ta ‘Musulman Duniya,’ wanda aka fi sani da MATW. Ganawar da aka yi da Mohamed Hoblos mai taken “Baiwa da Ciwon daji” ta ba da ƙarin tallafi ga ƙungiyar sa ta alheri. Aiyukan sadaukarwarsa ya fara ne Daga Kasar Togo amma ta bazu zuwa wasu ƙasashen Afirka kamar Burkina Faso, Ghana da Benin. Yana Zuwa ne don taimaka wa mabukata a kauyuka, wadanda suka hada da gina rijiyoyin ruwa, wuraren ilimi, ci gaban al’umma da ayyukan samar da kudin shiga, taimakon abinci, baya ga gina makarantun marayu, da Bayar Da kayayyakin Sana’o’i ga mata zawarawa da ‘ya’yansu da kuma ginawa da gyara masallatai.
Bayan gina muhalli ga ‘yan sansanin gudun hijira, Marigayi Ali Banat, kan samu lokaci domin kasancewa tare da yara dake sansanin da kuma yin wasa dasu ko cin abinci tare.
Ya kamu da cutar kansa a cikin 2015 kuma ya mutu a ranar 29 Mayu 2018 bayan fama da ciwon na shekaru 3. Ya bar saƙon ban kwana na ɗan gajeren lokaci kafin mutuwarsa.
wannan Rubutu Anyishi a Rariya