Bani Da Lafiya Kashi Na Sha Biyar (15).

0 539

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Abu Ruwaihah yasamu wuri ya zauna sai yake cewa: Wato Abu Labeeba yarinyar nan ta ka tana fama ne da Kambun baka kuma da alamu ma akwai sihiri a jikin ta.

Abu Labeeba yace: Subhanallah! Ni kuwa a ina yarinyar nan ta samo Kambun bakan nan, wato ni dai tunda take da matsalar nan bata tabayin yadda tayi a yau din nan ba wallahi.

Abu Ruwaihah: Au wai kana nufin irin wannan yanayin yau ne kadai tafara yinsa?

Abu Labeeba: Kwarai kuwa, yau din ma daga zuwa gidan kitso sai kawai mukaga an kawo mana ita a haka ba lafiya.

Abu Ruwaihah yace : Yauwa, to ka ji inda ake kyautata zaton ta gamu da kambun-baka din nan, domin wuraren nan ana yawan haduwa da kambun-baka amma mutane sunki ankarewa, sai kaga kowacce ta saki jikinta a wurin tana fitar da jikinta yadda taga dama, wurare ne kamar haka:

  • Wurin kitso
  • Wurin zanen Lalle ko ƙunshi
  • Wurin kwalliyar Make-up.
  • Gidajen biki (Musmaman ma ga wacce take bayyanar da kwalliyar ta.)
  • Kasuwanni

Da sauransu….

Abu Labeeba: Tabbas kuwa ka ga duk wuraren nan da ka lisaafo wurare ne da ake bayyanar da abubuwan da Addini yayi hani da a bayyana su.

Abu Ruwaihah: Ai duk abinda Addini yayi mana hani akai, domin amfanin kanmu ne da kuma kariyar lafiyar mu da zaman lafiyar, amma sai kaga munayin kan-taafi da hakan.

Ummu Labeeba dai tana can gefe tana jin duk abinda ke faruwa, ita kadai sai cewa tayi: Allah mai iko, gaskiya dai maganar mutumin nan haka take, domin mu mata fa kam sai ahankali akwai mu da shirme da shiririta, a karshe kuma iska lalura ta kama mu suka ido ya raina fata. Allah ya yafe mana.

Abu Ruwaihah ya mike zai tafi gida sai yace wa Abu Labeeba: Au ina bakin misk da jan misk din da nace ka siyo fatan dai anyi mata amfani da su ko?

Abu Labeeba: A’a wallahi, da wai na bari ne sai zuwa dare tukunna sai nayi mata amfani da shi kuma sai nazo natarar da yanayin nan da take ciki.

Yauwa dama ka ga kuwa ina son kayimin karin bayani akan maganin dangane da guraben alwalar da kace a shafa shi misk din, shin duk inda ake wankewa a alwala kake nufi ko dai wasu wurare ne dabam ba duka ba?

Abu Ruwaihah: Eh lallaikam nima na manta ne nayi maka bayani akan haka saboda nasan za ka nemi karin bayanin.

Wato inda ake shafawa su ne kamar haka: Kai da goshi, shaƙar hanci, kunnuwa, hannu izuwa hammata ( har tsakanin yan yatsu), kafafuwa da tsakanin yatsun kafa da kuma cibiya da kasan cibiya da mara da gefen al-aura amma kar a sanya a cikin al’aura sbd yana haifar da infection da kuma wasu kwayoyin cututtukan dabam kuma saboda an tofa Ayoyin Alqur’ani ne a ciki ba damar a sanya a cikin al’aura.

Abu Labeeba: Alhamdulillah, ka ga kam sai yanzu nakara fahimta, ALLAH dai yasaka da alkhairi kuma yakara basira Mallam.

Amma yanzu dai Duba Labeeba ka gani ta farka kuwa, Abu Ruwaihah yace da Abu Labeeba.

Abu Labeeba yaje ya duba ta yaga har yanzu dai cikin baccin take ba alamar tashi yanzu, sai ya dawo yace:

“Ai wato Abu Ruwaihah, gaskiya har yanzu baccin take yi bata tashi ba ma.”

Abu Ruwaihah yayi murmushi yace: Alhamdulillah, wato dama duk wanda akayiwa wanka da ganyen magaryar da yake dauke da karatun Alqur’ani ko wasu magungunan da basu sabawa hanyar Allah da ManzonSA ba ( waɗanda Allah ke kimsa ilimin haka ga wasu daga cikin bayinSA) ko kuma yasha, to daya daga cikin alamun da ake iya gane Kambun-baka ko sihiri ko mayu sun sake mutum shi ne: Za kaga ya yi wani dogon bacci bayan kammala wanka da shan maganin.

Abu Labeeba ya rike baki yana mamaki, sai yace: Ikon Allah kenan, To amma mallam ya nake ganin wasu sai kaga suyi tayin irin wannan wankan da magarya kuma su tofa Alqur’ani a ciki, amma sai dai kaji shiru ba labari. Shin kodai Ayoyin ne akwai wadanda ake karantawa ne na musamman ko kuma ya batun dai yake ne ?

(Insha ALLAHu a rubutu nagaba za muji ci gaban bayanin)

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.)

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »