Bani Da Lafiya Kashi Na Sha Shida (16)

0 520

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Abu Ruwaihah yadafa kafadar Abu Labeeba cikin murmushi sai yake ce masa: Wato, shi dai Alqur’ani gaba dayansa waraka ne daga dukkanin wani ciwo ko cuta da izinin Allah, amma kuma yana yin tasiri ne gwargwadon imanin zuciyar mai karanta shi domin magani da kuma zuciyar wanda za a yiwa maganin ta hanayar da ta dace da koyarwar Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama.

Abu Labeeba: Kenan tasirin irin ruqyar nan da ake yi da ganyen Magaryar asha kuma ayi wanka yana da alaqa da imanin da mutum yayi da Alqur’ani wajan zama silar samun waraka?

Abu Ruwaihah: Kwarai kuwa, ai ba ma iya na magaryar ba kawai, hatta duk wani magani ko tofin da ake tofa Alqur’ani a cikinsa matukar mutum bai girmama Alqur’anin ba kuma bai bashi girma da cancantarsa ba, to ina tabbatar maka babu yadda Allah zai sa karatun Alqur’anin nan yayi tasiri ajikin mara lafiyar, saboda ba’a baiwa Allah cancantarSA ba matuƙar cancanta.

Abu Labeeba: Masha ALLAH, Allah yakara tsare mana imaninmu. Amma mallam shin akwai wata sura ne ko kuma Ayoyi na musamman da aka ware su ne da ake karantawa marasa lafiya ko ayi ruqyar da ake yi da ganyen magaryar da su ?

Abu Ruwaihah: Ai shi Alqur’ani gaba dayansa waraka ne daga Fatiha har Naasi. Sai dai wasu malamai sun ware wasu Ayoyi ko surori (amma bai zama lallai ilalla su ne kadai ake iya karantawa ba), wadanda kuma na kawo su a cikin rubututtukan nan kamar haka:

1- BAMBANCI
2- MAFITA
3- SHIN JINNU ZA SU IYA RABUWA DA NI ?

Abu Labeeba: Masha Allah, wato kenan duk mai bukatar su yaje ya binciko rubututtukan nan, zai samu mafita Insha ALLAHu ?

Abu Ruwaihah: Kwarai kuwa, da yaradar ALLAH, ko kuma ya tuntubi duk malamin da ya yarda da shi wanda yake masani ne a harkar ruqya amma irin wacce ta dace da Muslunci.

Ka ga ni bari yanzu na wuce gida saboda akwai wadanda ke tsumayi na acan yanzu haka, Abu Ruwaihah yake sanar da Abu Labeeba.

Abu Labeeba: To ba matsala Mallam, amma wato wannan dogon baccin ma da take yi yanzu haka ba wata damuwa bace kenan?

Abu Ruwaihah: Kwarai kuwa, kar a tashe ta sai ta tashi da kanta, sai a sanyata tayi alwala tayi sallah, Insha ALLAHu za ta samu lafiya.

Bayan fitar Abu Ruwaihah daga gidan kenan sai nan take Ummu Labeeba ta fito daga inda take zaune cikin murmushi tana cewa:

“Wato Abu Labeeba lallaikam wannan mutumin ya san harkar magani, saboda yadda yake yin bayanansa ma wallahi duk jiki na ya yi sanyi sosai.”

Abu Labeeba ya juyo ya fuskanci Ummu Labeeba yana murmushi sai yace mata: Ummu Labeeba kenan, wato abinda nake ta son ki fahimta kenan game da bambancin masu magani tun ba yau ba amma kin kasa fahimtata, amma yanzu Alhamdulillah naga kin dauko hanya.”

Ummu Labeeba: Wato Abu Labeeba lamarin nan nima fa ba wai na yarda da gurbatattun masu maganin bane 100% ba, saboda nima kaina na san illar su sosai, kawai dai ni ina so ne yarinyar nan ta rabu da matsalar nan da wuri a wuce wurin kawai daga mu har ita kowa ya huta.

Abu Labeeba: Allah Sarki mata kenan, Haba Ummu Labeeba ! Tayaya kinsan da matsala da kuma masifar dake tattare da abun nan amma kuma kike kokarin jefa kanki da mu cikin halaka haka, kawai kije kiyi asarar Imaninki a wurin.

Ki tuna da cewa fa bayar da lafiya da rashinta duk Allah ne ke da wannan ikon ba waninSA ba, duk wani magani ko mai magani ba su da wani karfi ki kwarewar warkar da kowa dole sai ALLAH yaga dama yake bayar da waraka da lafiya ga wanda yaso ya baiwa ita.

Ummu Labeeba ta rike baki tayi jugumm ta rasa abinda za ta ce, sai tsayawa tayi tana sauraron Abu Labeeba yana bayani, yaci gaba da cewa:

Shin idan Allah bai bayar da warakar ba waye ya isa yabayar da ita? Ki tuna fa babu wanda zai iya sanya rashin lafiya ga wanda Allah yabashi lafiya, kuma babu wanda zai isa ya warkar da wanda Allah bai warkar da shi ba.

Lallaikam matuƙar ana so a zauna lafiya kuma marasa lafiyar mu su rika samun lafiya to wajibi ne sai an dogara ga ALLAH an bashi cancantarSA a matsayin wanda SHI kadai ne ke iya bayar da lafiya da waraka ga wanda yaga dama ba magani ko wani mai magani ba.

(Insha ALLAHu za muji abinda yafaru a rubutu nagaba)

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.)

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »