Takaitaccen Tarihin Sheikh Abubakar Ahmad Gumi

0 1,046

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Sheikh Ahmad Abubakar Gumi malamin addinin musulunci ne, kuma tsohon hafsan soja mai mukamin kyaftin a makarantar horas da sojoji ta Najeriya (NDA). Shi ne Mufti kuma mufassir na yanzu a babban masallacin Kaduna wato Sultan Bello.

Ahmad Gumi shine babban dan marigayi Shaykh Abubakar Gumi.  An haife shi a jihar Kano a ranar 1 ga watan Oktoba shekarar alib 1960. Ya fito daga  zuriyar malaman addinin musulunci tare da mahaifinsa Alkalin Alkalai na farko na tsohon yankin Arewa, mahaifinsa ya taka rawa wajen musuluntar da yan Najeriya dake yankin Arewa karkashin Sir Ahmadu Bello.

Ahmad Gumi ya halarci Kwalejin tunawa da Sardauna (SMC) don karatun sakandare. Bayan kammala karatun sakandare ya samu shiga jami’ar Ahmadu Bello kuma bayan kammala karatun sa ya shiga makarantar horon sojojin Najeriya. Ahmad Gumi ya yi murabus daga aikin soja a matsayin Kyaftin sannan ya koma Saudiya don ci gaba da karatun addinin Musulunci a Jami’ar Umm al-Qura inda ya karanci Fikihu da Tafsiri. Abokan aikinsa a jami’ar sun hada da Abdur-Rahman As-Sudais, Saud Al-Shuraim. Yana kuma bada Tafsirin Ramadan na shekara shekara a Masallacin Sultan Bello Unguwan sarki Kaduna.

 Ya yi aiki a rundunar sojojin a Nigerian Medical Corp (NAMC) a matsayin jami’in lafiya kuma ba tabbas ba ne ya yi ritaya a matsayin kyaftin. Zato shine ya bar aikin soja.

Sakamakon rashin tsaro da ake fama da shi a duk fadin Najeriya, Ahmad Gumi ya yi kokarin tattaunawa da masu garkuwa da mutane domin su sauke makamai domin a samu zaman lafiya a Najeriya, ya kan shiga daji da dazuka yana kaiwa sansanonin ‘yan fashi da maboyarsu daban-daban, yana mai jan hankalinsu wajen mika wuya ga wannan wasiyya.  kuma kada su ci gaba da yin garkuwa da mutane ko kashe su don neman kudin fansa, kamar yadda Allah zai gafarta musu idan sun tuba.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »