Tarihin Sheikh Sani Yahaya Jingir

0 1,257

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Sheikh Sani Yahaya Jingir Malamin Addinin Musulunci ne da ke zaune a Jihar Filato, Shi ne Shugaban Majalisar Malamai ta Kasa, Jama’atu Izalatul Bid’ah Wa’Ikamatis Sunnah JIBWIS ta bagaren Jos.

A ranar 25 ga Mayu, shekarar 2015 an zabe shi a matsayin shugaban majalisar lokacin da aka yanke hukunci bayan taron majalisar a Jos wanda majalisar dattawan Ulama’u ta yi yayin da Sheikh Alhassan Saed Adam ya zama mataimakin sa. An yi zaben ne lokacin da majalisar ta rasa shugabanta Sheikh Zakariyya Balarabe Dawud.

Jingir yana gabatar da tafseer na Ramadan na shekara shekara a Jos, yana daya daga cikin fitattun malamai a Arewacin Najeriya. Jingir yana wa’azin koyarwa kan muhimmaci da fa’idar bayar da ilimi a tsakanin ‘ya’yan maza da mata.

Jingir ya kuma yi fatwa mai karfi cewa duk wanda ya danganta Ibrahim Inyass da Allah a cikin ibada to Kafiri ne. Jingir ya nuna mahimmancin azumin Sitta shawwal na tilas bayan azumin Ramadan.

Jingir yayi wahalar yin wa’azi ga yan Boko Haram ta hanyar kafircewa cewa aikin su na Jihadi bai dace da Shari’ar Musulunci ba. Jingir a lokacin bude masallacin Juma’a da ke saman tudun Zinariya a Arewacin Jos, ya gargadi masu garkuwa da mutane a fadin kasar nan da su nemi gafarar Allah, su kuma tuba, idan kuwa ba haka ba zai shirya addu’o’i da azumi na musamman har sai Allah Ya halaka su.

Gwamnatin jihar Filato ta kama Jingir bayan ya karya doka ta hana yin sallar juma’a a ranar 27 ga Maris, 2020, lokacin da dokar hana fita da kullewa da akayi kan  Kiristoci da Musulmin Najeriya da kada su yi sallar jam’i don gujewa yaduwar cutar Korona.

Jingir ya ce; An aiwatar da dokar Korona ne don hana Musulmi daga Sallah,  kuma a ranar Juma’a a gidansa da ke Jos, Jingir ya ce “Korona yaudara ce, farfaganda ce da nufin yakar Musulunci da kuma aiwatar da yakin tattalin arziki tsakanin China da Amurka”.

Ya kuma kira hankalin gwamnatin tarayya da na jihohi da kada a hana sallar jam’i a Masallatai, Jingir ya kuma ce “Ina kira ga hukumomin Saudi Arabiya da su bude manyan Masallatai a Makkah da Madinah domin Musulmai su kiyaye Sallah.”

Bayan dambarwar da akai dashi kan Korona, Jingir ya ba da sanarwar cewa zai bi dukkan dokoki da aiwatarwa da gwamnatin Najeriya ta bayar don magance cutar saboda ya fahimci cewa cutar ta gaske ce ba kamar yadda yake tunani a baya ba.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »